Mu Rika Yi Wa Nijeriya Addu’a

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Lallai akwai bukatar ‘yan Nijeriya su dage su rika yi wa wannan kasar tamu addu’a. Musamman idan muka yi la’akari da cewa, ba mu da wata kasa a doron duniya da ta wuce mana ita.

A dalilin wannan ne JARIDAR TANTABARA ke kira ga ‘yan kasa da mu yi la’akari da abubuwa muhimmai wurin amsa wannan kira namu na yi wa kasa addu’a. Yi wa kasa addu’a ce za ta taimaka mana wurin samun albarkatu wadanda za mu mora har ma wasu kasashen makwabtanmu da sauran duniya su mora.

A wannan lokaci da muka fito daga lokacin damina, addu’a ce kawai za ta taimaka mana wurin samun albarkar gona mai amfani kuma yalwatacce ta yadda za a wadatu har zuwa zagayowar wata damunar. Sannan kuma addu’ar za ta kiyaye amfanin gonakinmu daga kwari da fari da dai sauran ibtila’o’in da ka iya bijirowa.

Addu’a za ta kawar mana da damuwowin da suke addabarmu a matsayin daidaiku, da jam’inmu. Wannan kuwa ya shafi matsalolin tsaro irinsu garkuwa da mutane, safarar kananan yara, sace-sace, da sauran barna da muke fama da su.

Addu’a za ta haifar da hadin kai a tsakaninmu a matsayin ‘yan kasa. Wannan zai kawar da

Share.

About Author

Leave A Reply