Muna Goyon Bayan Buhari Kan Dakile Rashin Da’a A Soshiyal Midiya –Dr. Bature Abdul’azeez

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Wannan wata tattaunawa ce da Shugaban hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwar Nijeriya, DAKTA BATURE ABDUL’AZEEZ ya yi da MUHAMMAD ABUBAKAR kan shirin dakile kalaman batanci a kafafen sadarwa da gwamnatin Buhari ke son yi. Dakta Bature ya dauki lokaci mai tsawo yana bayar da kariya ga gwamnatin Buhari da taka burki ga duk wasu masu kokarin bakanta gwamnatin, a cikin gida ko daga waje. A cikin wannan tattaunawar ya yi bayanai masu muhimmanci sosai. Ga yadda hirar ta kasance:
Mene ne ra’ayinka dangane da lamarin fara bibiyar masu kalaman batanci a kafafen sadarwa da gwamnatin Buhari ke son yi?
Tun a 1983, a mulkin buhari na farko yake ta kokarin sassaita Nijeriya. Domin idan ba a manta ba, a wancan lokacin ne ya kawo wannan dokar ta ‘War Against Indiscipline’, wato yaki da rashin da’a. Yaki da rashin da’an nan saboda dogon lokaci da aka dauka, a can ya yi aiki ta yadda har sai da mutanen kasar nan suka yaba. Domin yadda komi ya dawo daidai. Toh kuma sai ya canza salo, yanzu sai aka yi yaki da masu maganganun da za su cutar da Nijeriya da ‘yan Nijeriya. Maganganun da kullum burinsu su hada rikici. Irin wadannan mutane ne suke hada rikicin kabilanci, wadannan masu maganganun tun daga kan tsofaffin shugabannin kasa, da jama’arsa da NGOs na waje da na cikin kasa sune ke tayar da irin wadannan maganganu na son shafawa Nijeriya kashin kaji. Ka ji suna cewa mu muka fi kowa rashin abinci mai gina jiki, mu muka fi kowa talauci. Kuma sai ka ga an samu wasu ‘yan Nijeriya marasa kishin kasa sun fara goyawa wadannan NGOs baya, wanda kowa ya san biyansu ake yi daga waje.

Kamar yaya kenan?
NGOs din nan, baragurbinsu a ciki, ba duka ba, da kuma miyagun ‘yan jaridu su yi abin da za su sa a soshiyal midiya don a yamutsa kasar. Za ka ga suna yafa maganar da suka ga dama a kan Nijeriya da gwamnati. Su yafar maganar da suka ga dama akan shugaban kasa. Mutanen nan na matukar bata min rai, suna damuna sosai. Amma wacce tafi damuna masu kokarin hada fitinar wargaza Nijeriya, wadanda dam aba Nijeriyar ba ce a gabansu. Tunda ba su samu mulki ba. Za ka ga masu irin wadannan maganganun za ka ga an yi barna a cikin kasa, amma irin mutanen nan ba za su fito su yi alhini ba, amma da zaran sun yi wa kasa zagon kasa an taba su, sai ka fara jinsu wai su masu kare hakkin dan adam. Ni Dakta Bature Abdul’azeez na ce, karya suke yi. Don ba su san komi dangane da Afirka da kasashenta ba. Duk wanda ke son wargaza Nijeriya sai dai shi ya wargaje.

Kenan wannan shirin na gwamnatin Buhari yana da tasiri?
Mu ai ma sai dai mu ce, muna matukar godiya ga gwamnatin Muhammadu Buhari ganin yadda suka kawo tsarin bibiya da magance kalaman batanci a Soshiyal midiya, wannan kuma zai shafi hatta ‘yan jarida masu yada farfaganda da karya. Duk wanda aka kama za a yi masa tara. Jama’a duk irin wadannan abubuwan da mutane suke yi a soshiyal midiya, kasashen turawa ba za su taba yarda da wannan shiriritar ba. Kasashen turawa duk irin wadannan farfagandar ta karya, babu ita a wurinsu. Duk wata babbar kasa ta Bature wacce ban je ba, sai kadan. Takamarka ka ce Ingila, Jamus Faransa, duk na je ba a haka. Ko takamarka ka ce Amurka, nan ma kusan shekarata 15 duk wannan abin da ake yi a Nijeriya da sunan ‘yancin dan kasa, babu a can. Duk ba a wannan a can, amma mu saboda wadansu tsofaffin shugabanni, irinsu wanda ake zugawa wai shi gwanki. Saboda Buhari bai yarda ya zama yaronsa ba, Buhari bai yarda a yi wani abu wanda za a dulmiyar da kasa ba. A kan wannan abin ne ya sa wannan tsohon yake yin duk wani abu don ya ga ya bata gwamnatin Buhari, toh wannan tsohon karyarsa, don muna nan, shekarunsa ma sauran kadan ya bar duniya. Ba wani ne zai kashe shi ba, Allah ne zai kashe shi, saboda zamansa a duniyar ma ba ya amfanar ‘yan kasa. Duk wani fadace-fadace da ake yi a arewa sun samo asali ne daga mulkinsa. A lokacin mulkinsa ne ya yi ta kokarin ganin ya raba arewa da arewa ta tsakiya. Da zimmar rikicin addini da kabilancin yare. Saboda haka muna goyon bayan buhari kan wannan tsari na dakile rashin da’a a soshiyal midiya.
Sai ka ga mutum ya saki baki ya fitar da maganar da kafin kwana uku an kaure da yaki a wani wurin. Mutanen nan da ake zaune da su, kowanne yare da ka ke ji a duniyar nan ta Allah, Allah ne ya yi su, don a fahimci juna. Kuma Allah shi ne ya yi addinan nan guda biyu. Ko kirista ko musulmi. Allah ya ce, idan da ya so sai ya sa jama’a su zama daya duk duniya ya zama musulunci ne kawai, ko duk duniya ya zama kiristanci ne kawai. Saboda haka ‘yan Nijeriya su fita harkar sauraron abin da zai mayar da mu baya. Mu fita harkar masu yada kalaman rashin da’a da batanci ga kasa, ko jama’a. Su masu yin haka burinsu shi ne a cinnawa kasar wuta kowa ma ta shafe shi. Akwai wani shugaba na Amurka da ya ce, shi tun da yah au shugabanci ya daina tura sojojin Amurka kasasa ana zuwa ana kashe su a banza. Ya ce, shi ko bai tura ba suna da ajandar daga kasarsu za su iya hargitsa duniya, kuma haka aka yi. Sun gane su kafa kungiyoyi da NGOs a ayi ta kunna wuta a kasashen duniya. Galibin wadannan NGOs din fuskarsu biyu ne. Don haka duk wanda aka kama da rashin da’a a hukunta shi kawai.

Share.

About Author

Leave A Reply