Muna Kira Ga Masu Amfani Da Twitter Da Su Zama Masu Kishin Kasa -Dr. Bature Abdul’azeez

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Wannan wata tattaunawa ce da MUHAMMAD ABUBAKAR ya yi da shugaban hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya, Dr. BATURE ABDUL’AZEEZ, inda ya bayyana abin da ya sa qungiyarsu ta ‘Patriotic Elders of Nigeria’ ta ke kira ga masu amfani da Kafar Twitter da ‘yan jaridar kasashen waje na su daina yin abubuwan da za su haifar da tashin hankali a Nijeriya. Ga yadda hirar ta kasance:

Me za ka ce kan janye dokar hana amfani da Kafar Twitter?

Toh, magana akan Tuwita wacce Mai Girma Shugaban Kasa ya dage dokar da ya kafa musu.

Saboda abin da ya sa, don an dage Tuwita, Tuwitar nan da aka dage ko asarar da aka yi a watanni bakwan nan, to dage tan da aka yi duk inda aka kai wata biyar tana aiki, da ku da kuke amfani da ita da gwamnati sai ta samu ninkin abin da take samu, domin da kudin da take samu a boye ba wanda ya san abin da take samu. ‘Yan Nijeriya don me za mu sa bukatarmu ko mu sa siyasa ko mu sa bangarenci, ya sa mutane su dinga magana kamar ta jahiliyya, ta tsananain kin kasa da tsananin kin kishin kasa.

Duk kasar da kuka sani a duniya tana da dokoki, tana da tsari wannan abin da ‘yan Tuwita suke yi idan ka kasa shi 10, wallahi ko kashi biyu basu isa su yi a Amurka ba, ko a Ingila ku masu amfani da Tuwita kun jahilci dokokin duniya da na kasashe daban-daban. Duk abin da Nijeriya ta yi don kare kasa don tattalin arzikin kasa, don zaman lafiyar kasa, baku da aiki sai hayaniya, sai maganganu zafafa, kuma ana cewa Nijeriya akwai ‘yancin fada a ji, to duk ‘yancin da zai zama zai cutar da tattalin arzikin kasa, zai cuyar da kokarin da ake yi a kasa. To wannan ‘yanci idan ba kishin kasa, a sakin layi na 39 na kudin tsarin mulkin kasa, kuma an kulle shi a sakin layi na 45 na kundin kasa, saboda akwai ka’idojin da ko Nijeriyar da aka ce mutum yana da ‘yancin fada a ji, in ka koma shafi na 15, ya yi magana da ina da ina ya kamata mutum ya dinga magana, ba ko ina da ya kamata mutum ya rika magana ba.

Ko akwai karin bayani?

Dan Nijeriya bai da damar da zai rika zagin sojoji ko ‘yan sandan kasa, ka ga mutum yana zagin tsaron kasa, zagin tsaron kasar nan da za ka ji suna ta magana, za ka ga idan aka kirawo shi ya zo ya ba da kansa don tsaron kasa na kwana bakwai, wallahi ba zai iya ba, ba zai taba tunanin ma zai zo don ya kare kasarsa ba, amma mutane malama an gina Nijeriya a kan kishin kasa, kuma wadanda suke zantuka irin wadannan sun samu dama ba’a ce musu komai.

To ya kamata masu irin wadannan maganu marasa da’a ya kamata gwamnati ta rika sa ido a kansu, da yawansu ‘yan jam’iyyar adawa ne, ba sa duba kasarsu siyasarsu suke dubawa, da yawansu mutane ne da yawancinsu wallahi ba su da sana’ar yi ma sai da Tuwitar nan ta shigo, a kulla ko wane sharri na cutar da kasa, da zai cutar da tsaron kasa, da zai cutar da tattalin arzikin kasa, da shi suka samu kudin da shi suke kokarin su kare Tuwita, sun san kudin da suke biya a sauran kasashen duniya, kun san ko wace kasa irin tsare-tsaren da kowace kasa ta gindaya musu.?

Kasashe nawa ne suka rufe Tuwita, kuma ana ji ana gani  ana gani dole aka kyale su kuma har yanzu basu bude ba. Yanzu da aka ce an tsare su biya haraji, to yanzu ba kasarmu zai amfana ba, kudin harajin kuma da za su biya, ko cewa aka yi su ba da kashi 15 cikin 100, in ka ji kudin da suke samu sai ka yi mamaki. Don rainin wayo masu Tuwitar nan cewa suka yi Shelkwatarsu ba za su ajiye ta a Nijeriya ba, a takaice suka dauke ta suka kai ta Ghana.

Amma haka kawai yara ‘yan YAHOO su rika shiga saboda a nan suke aikace-aikacensu na cinikin kwaya da harkar kudin jabu da sauran miyagun laifuka, da sauran rigingimu da ake yi a kasarmu Gabas da Yamma Kudu da Arewa, da yake ta nan ne suke samu suke kunna wutar fitina, a kaice ka ji suna fada kamar wadanda suke wani ‘yanci na fada, ai ‘yancin fadar albarkacin baki yana da iyaka a kowace kasa a duniya

Dazu ina jin Balarabe Shehu Illela, kai na ji kwarai da gaske saboda ya fito ya wanke wannan dan jaridar na BBC. Me ya sa ‘yan Nijeriya masu aiki a BBC suke son cusa kasarsu cikin rikicin tashin hankali, cikin yamutsi ko da wane lokaci sun fi goyon bayan barna? Ya kamata su yi koyi da ‘yan jaridun Nijar. Dan jaridar Nijar za ka ji wallahi ko wace mahana ce ta tasowa kasarsa ya san wane irin jagoranci zan yi mata, ya kwantar da hankalin mutane ya fadakar da gwamnati abin da ake bukata.

Wanne sako ka ke da shi daga karshe?

Kai mai magana ka san irin abin da za ka fada, duk irin wadannan maganganun da kuke a sauran kasashe, da Balarabe yake cewa ba zai fada ba. Allah wallahi na san akasashe sun fi 20 in mutum ya yi wannan in mutum ya fad aba ma a kurkuku zai kwana ba a lahira zai kwana.

Ya za ai a kasa saboda an ce an bar ‘yancin fadar albarkacin baki, ai ba hauka bane, kuma ‘yancin fadar albarkacin baki ai ba kasar aka ce a sayar ba, bakin naka in ya fada ba cewa aka yi ka sayar da kasar ba, kuma ba so a ke ka sayar da zaman lafiyar kasar ba, kuma ba so ake ka kushe duk kokarin nan da ake yi saboda kai dan abin da za ka samu, dan abin da za ka samu nawa yake, dan cikin cokali ne.

Ku ‘yan Tuwita din ai gaba daya idan aka tara ku wadanda kuke cin abinci da Tuwita ko dubu daya baku kai ba, ku tuna fa Nijeriya mutane ne a cikin sama miliyan 200, kuma da wannan Tuwitar babu abin da ba’a tufka ba don a cutar da mutane

Share.

About Author

Leave A Reply