Musulunci Ya Amince Da Tsarin Tazarar Haihuwa, Cewar Imam Hussaini Ningi

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

HUSSAINI SHEHU IMAM, Babban Malamin ne addinin Islama ne da ke karamar hukumar Ningi, wadda ya wakilci babban Limamin Ningi a yayin ganawa da ‘yan jarida masu aiki kan lafiyar al’umma a wani ziyara da suka kai Ningi, ya shaida cewar tsarin bada tazarar haihuwa abu ne wadda addinin Musulunci yayi na’am da shi, yana mai cewa Musulunci ya umurci a baiwa jariri cikakken shayarwa a duk lokacin da aka haife shi. KHALID IDRIS ya kasance a wajen ga kuma hirar yadda ta kaya:

Ka gabatar mana da kanka?

Hussaini Shehu Imam, nine wakilin babban Limamin Ningi a nan wajen.

Wani irin rawa malamai ke takawa a wannan batu na bada tazarar haihuwa?

Da yake tun usuli addinin Musulunci ya zo da nasa tsarin wadda in ka kalli abun za ka ga akwai shirin bada tazarar haihuwa musamman a inda Allah ya yi magana a kan shayarwa; shayar da yaro a matsayin cikakken shayarwa shekara biyu. To, ka ga duk yaron da aka samu shayar da shi na tsawon shekaru biyu to lokacin da za a sake samun juna biyu ka ga an samu tazara a tsakanin shayar da wannan yaron da kuma sabon jaririn da zai biyo bayan shi.

Kuma shi addinin Musulunci ya daura nauyin kula da mahaifiya tun daga samun cikinta har zuwa lokacin da za ta yaye jaririnta hakkin hakan na kan mahaifi ne. Idan har maza suka san wajibcin shayarwa da dawainiyar da ke kansu tun daga samun ciki har zuwa haihuwa, har zuwa shayarwa har bayan shayarwa to lallai zai ke kula domin a lamarin akwai bangaren da uwa ta dauka akwai bangaren da uba ya dauka, shi wannan lamarin, lamari ne da yake tsakanin ma’auta biyu. Idan kowa ya sauke nashi nauyin za a samu zarafin baiwa yaro cikakken shayarwar da addini ya umurta.

Amma wasu jama’a ba su san da hakan ba wasu matakai kuke bi wajen koyarwa ko fadakar da su kan hakan?

Eh to muna iya kokarinmu wajen ilmantar da jama’a abin da shari’ar Musulunci ya tanadar. Daman shi Musulunci ba kin abu yake yi gaba daya ba, ba kuma amincewa da abu yake yi gaba daya ba, yana kallon idan ya zo daidai da abin da yake asali a shari’a to babu wani matsala, to shi tsarin tazara kamar yadda na fada maka in aka bi cikakken umurnin shayarwa lallai za samu tazara a cikinsa. Don haka muna iya kokarinmu wajen wayar da kan jama’a kan shi tazara din don su gane halascin shi a shari’ance.

Masu sukar tsarin bada tazara kenan kana ganin akwai rashin sanin addini a tare da su?

Kwarai da gaske, akwai rashin sanin addini sosai, saboda akwai hadisai da dama da suka yi magana a kan Azalu a zamanin Manzon Allah (S) wadanda idan ka kalli su wadannan Hadisan sun yi magana ne a kan wani abu mai kama da bada tazara din. Don haka fahimtar addini shi kanshi da fahimtar yadda rayuwa take yana dada fito da abubuwa a fili, sannan masana, malamai sun yi rubuce-rubuce a kan wannan bangare sosan gaske, don haka masu suka ina ga iliminsu ne bai kai wajen ba. Daman shi mutum yana jahiltar abin da bai sani ba.

Yanzu ya yanayin amsar tsarin bada tazara a tsakanin jama’a tun da gashi ku malamai kun shigo don wayar da kan jama’a?

Alhamadullahi, akwai ci gaba matuka, domin mutane suna ganin hatsarin da suke fadawa a tsakanin haihuwa barkatai, ka ga mace tana Da dan wata shida sai ta je ta sake samun wani juna biyu, kuma sai ka ga yadda za a yi da wannan jaririn da shi wannan da bai zo ba sai ka ga an shiga wani yanayin da hausawa ke cewa rayuwar guzuma ko uwar ta mace, ko shi jaririn farkon da aka haifa ya gaza samun shayarwa mai inganci da shari’a ya nemi a yi irin haka sai ka ga rayuwar yaro ya zama abin tausayi wadda musulunci bai amince a jefa kan cikin kunshi ba. Shi dai musulunci ya nemi a baiwa yaro cikakken shayarwa wadda idan ma’autara suka sauke wannan nauyin sai a ce masha Allah.

Idan ya zama mace tana son ta bada tazara a tsakanin haihuwar da take yi, shi kuma mai gidanta ya hana, ya hakan yake a shari’a?

Shi mas’alar aure guri biyu, akwai wurin da hakkn mace ce dari bisa dari, akwai kuma wajen da hakkin na mijin ne dari bisa dari. Akwai kuma babin da za su zo su tattauna a tsakaninsu. Allah (T) ya yi magana cewa idan mace ta zo Yayen yaro su tattauna su yi shawara a tsakanin matan da mijin. In dai har za su tattauna kan lamarin da ya shafi yaron haka ma renon yaro ba lamari ne da mutum daya zai yanke hukunci a kai ba, sai sun zauna sun baiwa kansu shawarorin yadda za su yi.

Awesome
  • User Ratings (0 Votes) 0
Share.

About Author

Leave A Reply