Na Gaji Da Surutan Banzan Da A Ke Yi Min A Barcelona, Inji Messi

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Shahararren dan kwallon kafa, kuma gwarzo a duniya, Lionel Messi ya ce ya gaji da irin gutsiri-tsoman da ake ta faman yi a kansa a Barcelona.

Messi ya bayyana haka ne a jiya Laraba, bayan da wani tsohon dillalin Griezman ya zargi Messi din da laifin rashin dafa wa dan kwallon na kasar Faransa tun bayan dawowarsa Barcelona daga Atletico Madrid.

Messi ya ce, duk wani surutun banza da aka yayibo a Barcelona shi a ke dora wa laifi.

Wannan na daga cikin dalilin da ya sa Messi din ya ji gabadaya kungiyar ta fice a ransa, inda ya so ya barta a kwanakin baya.

Cikin wadanda suka nemi sayen Lionel Messi akwai Kungiyar Kwallon kafa ta PSG da ke taka leda a Kasar Faransa.

Wani karin abin takaici da Messi ya bayyana shi ne yadda hukumomi a Sipaniya suka takura masa da batun haraji. “Na kwashe awa 15 cikin jirgi, daga Argentina zuwa Sipaniya. Amma ina dawowa sai na taras da jami’an amsan haraji suna jirana. Wannan matsa lamba har ina?” inji shi

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply