Na Rantse Ba Zan Ba ‘Yan Manchester United Kunya Ba, In Ji Cavani

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Sabon dan wasan gaba da Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sayo, Edinson Cavani ya sha alwashin cewa ba zai ba Kungiyar kunya ba.

Cavani ya ce, zai mutunta lamba bakwai da aka ba shi, kuma zai yi mai yiwuwa wurin taka leda a Gasar Firimiya.

Manchester United dai ta sayo Cavani ne daga Kungiyar Kwallon Kafa ta PSG da ke Kasar Faransa.

Kungiyar ta Man. United da magoya bayanta suna sa ran cewa, Cavani zai iya fitar da su daga kunci da Hukuncin da suke amsa a wasanninsu.

A cikin wannan watan ne cinikin Cavani ya fada kafin a kulle Kasuwar saye da sayar da ‘yan wasa.

Share.

About Author

Leave A Reply