NAERLS Ta Bukaci Karin Zuba Jari A Noman Rani Don Kaucewa Karancin Abinci

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Cibiyar wayar da kan manoma NAERLS, da ke Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria ta bukaci gwamnati ta kara zuba jari a bangaren aikin monan rani a fadin tarayyar kasar nan.

Shugaban cibiyar, Farfesa Emmanuel Ikani, ya bayyana haka a tattaunawarsa da manema labarai a garin Zaria ranar Alhamis, ya kuma kara da cewa, hakan zai rage irin asarar da manoma ke tafkawa da rage karancin abinci da ake fama dashi a fadin kasar nan.

Ikani ya kuma bayyan cewa, ana asarar fiye da kashi 30 na kayan da aka noma saboda yadda aka kasa tanadar kayan noman, akan haka ya ce, yakamata a samar da hanyoyi na zamani da za a rinka ajiyar kayan da aka noma don amfani da su anan gaba.

Ya kuma bayyana cewa, in har ana son kaucewa irin wanna asarar ya kamata a rungumi noman rani don samar da cigaba yadda ya kamata hakan kuma zai kara wa manoman kudaden shiga.

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply