Nasarorin Bichi A Hukumar DSS Cikin Shekara Biyu, Daga Gidado Ibrahim

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daya daga cikin dalilan da ya sa ake bibiyar mutum ko yi masa jarabawa shi ne don a gane irin nasarorin da ya samu ko akasin haka. A lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Yusuf Magaji Bichi a matsayin Darakta Janar na DSS, sashen rundunar tsaron na cikin wani yanayi na bukatar gyara.

Hukumar ta DSS tana cikin kishirwan shugaba mai kamala, kaifin basira, kwarewa da karfin hali a fagen aiki, wanda zai dawo da martabar hukumar kamar yadda take a baya.

Ana cikin irin wannan halin ne, sai Shugaba Buhari wanda ke da hangen nesa wurin iya zakulo ma’aikata, ya nemi Yusuf Bichi da ya dawo aiki daga ritayar da ya yi domin farfado da darajar wannan hukuma ta DSS. Ai kuwa yanzu da ake cika shekara biyu, an ga irin aikin wannan kwararren mutum a Hukumar DSS.

Idan muka waiwaya baya cikin wadannan  shekaru biyu, za mu ga tarin abubuwan da Yusuf Bichi ya kawo a tsarin gudanarwa da aikin jami’an DSS a fadin Nijeriya.

Ko ina sai sam barka da tofin fata nagari ake yi, wanda kafin zuwan Bichi sai da darajar Hukumar DSS ta kusa yin faduwar bakar tasa. Yau DSS ta zama samfuri wurin yin kwatance a aikin da ya dace tsakanin sauran bangarorin gwamnati.

Wannan ne ma ya sa wata kungiya a Geneva ta ba Yusuf Bichi lambar yabo. Bayan zaben shekarar 2019, wata kungiyar sa-ido kan harkar zabe mai suna ‘Human Rights Commission’ wacce ke Geneva ta kasar Switzerland ta ba shi wannan lambar yabon. Kungiyar ta ce, an ba Bichi lambar yabon ne saboda irin rawar da ya taka wurin tafiyar da hukumar DSS a yayin gudanar da zaben.

Hukumar Tsaro ta farin kaya (SSS) wacce a yanzu aka fi kira da DSS, ita ce ta farko wurin tabbatar da tsaro a cikin gida Nijeriya. Hukuma ce da babban aikinta shi ne tattara bayanan sirri a fadin Nijeriya, domin tabbatar da tsaro da kariya ga kasa, Shugaban Kasa da sauran manya masu rike da madafun iko. Wannan hukumar ta DSS ta bubbugo ne daga tsohuwar hukumar tsaro ta ‘National Security Organization, wacce aka rushe a shekarar 1986.

A zamanin mulkin soja na, Ibraim Badamasi Babangida ne ya yi amfani da kundin tsarin mulkin soja na 19, a watan Yunin 1986 wurin rushe hukumar tsaro ta ‘National Security Organization’, inda ya fasata gida uku, daga ciki aka fitar da SSS wanda sun eke da alhakin kula da tattara bayanan sirri na cikin gida Nijeriya. Sai Hukumar NIA (National Intelligence Agence) wadanda ke da alhakin kula da tattara bayanan sirrin kasashen ketare don kiyaye martabar Nijeriya. Sai kuma Hukumar DIA (Defence Military Intelligence) wadanda ke da alhakin kula da bayanan sirrin soji a cikin gida da wajen Nijeriya.

Daya daga cikin manyan manufofin DSS shi ne tabbatar da tsaro ga Nijeriya, daga fadawa tarkon kutsen masu kutse na cikin gida ko na waje. Sannan kuma tare  da tattara bayan sirri wadanda da su suke amfanin wurin tabbatar da tsaron kasa, shugaban kasa da sauran masu rike da madafun iko. Sune a gaba wurin fallasa wasu muhimman tuggu da ‘yan ta’adda ke kullawa Nijeriya.

Wani abin burgewa da shugabanci irin na Yusuf Bichi shi ne kiyaye mutuncin ma’aikatansa da riko da gaskiya. Ya dawo da akidar rike sirri a hukumar DSS, ta yadda yanzu jami’an DSS sai su gudanar da ayyuka muhimmai ba tare da kowa ma ya sani ba.

A lokacin da aka nada Magaji Bichi a matsayin Daraktan Hukumar ta DSS, fadar shugaban kasa ta ayyana shi a matsayin shahararren masanin tsaro kuma kwararre. Wannan kadai ya ishi zama dalilin da za a ce, gwamnatin Buhari ta yi amfani da cancanta wurin zakulo shi tare da ba shi wannan mukamin.

Tun bayan shigarsa ofis a matsayin Daraktan DSS, Yusuf Magaji Bichi ya cimma nasarori masu tarin yawa, wadanda suka saita hukumar ta DSS zuwa hanya ingantacciya. A lokacinsa Hukumar DSS ta yi namijin kokari wurin haifar da cikas ga masu garkuwa da mutane, ‘yan ta’adda da sauran mamuguntan da ke addabar ‘yan Nijeriya.

A karkashin shugabancin Bichi, yanzu hukumar DSS na matukar yin biyayya ga hukuncin kotu domin kiyaye martabar dimokradiyya, ba kamar yadda shugabannin hukumar na baya suka yi ta aikatawa ba.

Magaji Bichi ya fara aikin DSS ne tun lokacin da hukumar tsaron ke ‘Nigerin Security Organization’, wanda daga cikinta ne aka tsamo DSS din. Ya samu horo akan sarrafa bayanan sirri, iya kula da daukar sabbin ma’aikata a Kasar Ingila da kuma a nan gida Nijeriya.

Daraktan na DSS ya shiga ofis da sabbin tsare-tsare na inganta aikin hukumar, ta yadda ya fadada harkar tattara bayanan sirri, sarrafa bayanai, daidaita lamurran da suke neman jagulewa, binciken kwakwaf, atisayen daidaita lamurra, da dai sauran wasu fannoni.

A farkon fara aikinsa na DSS, Yusuf Magaji Bichi ya yi aiki a matsayin Daraktan DSS na Jihohin Jigawa, Neja, Sakkwato da kuma Abiya.

Haka kuma a baya ya taba rike mukamin Daraktan dake kula da Majalisar Kasa, Darakta a hedikwatar kasa ta tabbatar da tsaro, daraktan gudanarwa, daraktan tattara bayanan sirri, daraktan bibiya da kuma daraktan kudi duk a hukumar DSS din. Haka kuma ya yi darakta a Makarantar Hukumar Tsaron farin kaya.

Wadannan wasu nasarori ne da ba za a iya kawar da kai daga gare su ba. Abu daya ya kamata gabadayanmu mu taimaka mishi da shi, shi ne hadin kai domin tabbatar da zaman lafiya a Nijeriya.

– Ibrahim shi ne Daraktan Sadarwa da tsare-tsare na kwamitin tallafawa Shugaban Kasa ‘Presidential Support Committee’ (PSC).

Share.

About Author

Leave A Reply