NDE Ta Horas Da Matasa Dabarun Kawata Muhalli A Jihar Kebbi

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Hukumar samar da ayyykan yi ta kasa, NDE ta fara horas da matasa 42 dabarun kawata muhalli a jihar Kebbi.

Shugaban hukumar, Mallam Abubakar Nuhu-Fikpo ya bayyana haka a taron kaddamar da matasa masu karbar horon a garin Birnin Kebbi ranar Asabar.

“An shirya horaswar ne don rage matasa masu zaman kashe wando wadanda suka kammala makaranta kuma suke neman aiki yi a fadin jihar.

“Shirin zai taimaka wajen kawata manyan biranen jihar, ta haka kuma an samu yanayin kare muhalli wanda haka kuma zai taikmaka wajen kare kwararowar Hamada a fadin jihar,” inji shi.

Ya kuma ce an samar da matasan ne daga kananan hukumomin jihar guda 21 inda aka dauko mutum biyu daga kowanne karamar hukumar.

Shugaban hukumar wanda ya samu wakilcin Alhaji Abdullahi Danjuma- Machika shugaban hukumar a jihar ya kuma bukaci matasan su dauki abin da ake horas da su da mahimmanci.

Ya kuma shawarci matasan su bi dukkan dokokin da aka sanya na horaswar da mahimmanci a tsawon zaman su.

Daya daga cikin matasan da suka amfana, Muhammad Usman ya godewa hukumar NDE da suka samar musu da shirin horaswar, ya kuma ce, lallai za su amfana kwarai da gaske.

Share.

About Author

Leave A Reply