NEMA Ta Bayyana Kananan Hukumonin Da Ke Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa A Jihar Sakkwato

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A ranar Talata ne hukumar bayar Da Agajin Gaggawa, NEMA ta ce wasu kananan hukumomi a jihar Sakkwato na fuskantar matsananciyar barazanar ambaliyar ruwa a wannan shekarar.

Shugaban hukumar ta NEMA, AVM Muhammadu Mohammed ya bayyana haka a yayin da tawagarsa ta ziyarci Bataliya na 26 na rundunar Sojin Nijeriya a barikin Ginginya da ke Sakkwato.

Ya kuma kara da cewa, kananna hukumonin da suke fuskantar barazanar ambaliyar sun hada da Goronyo, Sokoto North, Sabon Birni, Rabah, Isa, Sokoto South, Dange-Shuni, Kware da kuma Wurno.

Shugaban hukumar ya samu wakilcin darakta mai kula da ayyuka na musamman a hukumar, Joseph Akujobi, ya kuma ce, ambaliyar na barazana ga harkokin noma a jihar.

“Mun kawo ziyara ne don a fadakar da al’umma akan ambaliyar da ake fuskanta jihar, hakan kuma yana barazana ga ayyukan samar da abinci a jihar.

“Ambaliyar ruwa a kasar nan ta fara zama ruwan dare musammna tun bayan da aka samu ambaliyar ruwa a shekarar 2012 an kuma samu wata ambaliyar a shekarar 2018, wanda hakan ya sa aka ayyana dokar ta ba ci a wasu jihohin kasar nan.

Akan haka shugaban hukumar NEMA ya bukaci hadin kan dukkan masu ruwa da tsaki don rage irin asarar da za a tafka in ambaliyar ta auku da kuma samar da yadda za a kai agajin gaggauwa ga al’ummar da suka samu kan su cikin ambaliyar ruwan.

A nasa martanin, Shugaban Bataliya na 26, Lt-Col Usman Mohammed ya ce, rundunar sojin Nijeriya na bangare na musamman na kai agajin gaggauwa in ana samu barkewar annoba.

Ya kuma godewa shugaban hukumar, ya kuma yi alkawarin bayar da dukkan goyon bayan da ake bukata.

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply