Nijeriya Ina Muka Dosa?

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Ado Umar Lalu Da Shamsu Mohammed Funtua
Burin kowane dankasa shi ne ganin ci gaban kasar sa a dukkan fannonin rayuwa ta yadda za a samu walwalar yan ‘kasa da ci gaba mai dorewa. Wannan fata yana kaiwa ga nasara idan kowane dankasa daidai kun mu ko kuma al’umma sun sa kishin kasa ta yadda za su shimfida tsarin gwamnati cikin adalci da sl zai samar da kyakyawan shugabanci.
Duk inda aka sami kyakkyawan tsarin rayuwa da shugabanci, kowane dankasa kokari yake yaga yabar wani abin tunawa da yan baya za su gani suyi alfahari dashi kuma ya zama abin koyi gare su.
Irin wannan tsari bazai taba samuwa ba idan kishin kasa yayi karanci a cikin al’umma da sannu sai gurin gina kai ya mamaye gurin gina kasa ta yadda za a raunana tsarin tafiyar da al’umma da za su haifar da dinbin matsaloli da za su dauki dogon zango kafin a magance su ko kuma sukai ga rushewar al’umma wanda shi ne halin da mu ke ciki a wannan kasar tamu dake haifar mana da koma baya a dukkan fannonin rayuwar mu na yau da kullum.
Duk wani bangare da muka dauka tun daga bangaren ilimi, tsaro, kiwon lafiya, shari’ah, ruwan sha, sufuri, ayyukan gona, kudi da sauran bangarori dukkan su suna fama da matsaloli iri daban-daban da sukayi masu tarnaqi sakamakon son zuciya da aka saka wajen tafiyar dasu.
A kullum a Nijeriya saboda sanya son zuciya da muka saka wajen tafiyar da harkokin mu da kuma amanar da aka dora mana yasa kasashen da basu kaimu ba a baya yanzu suka wuce mu sukayi mana fintinkau saboda kishin kasa da suka sanya a zuciyar domin ciyar da kasashen su gaba.
Mun sami kammu a cikin wani yanayin na zargin juna da kuma take laifukan mu, mu rinka kallon laifukan wasu.
Tabbas gyaran Nijeriya ya fi karfin duk wani mahaluki shi kadai dole sai yan siyasa, yan kasuwa, sarakuna, malamai da talakawa kowa sai ya bayar da gudunmuwa irin tasa domin ceto Nijeriya kafin ta dukkushe. Kamar yadda bahaushe ke cewa hannu daya baya daukar jinka, haka kuma hannu da yawa maganin kazamar miya.
Dolen mu ko muna so ko bama so sai mun dawo turbar gaskiya da adalci a cikin al’amurran mu na yau da kullum ko kuma matsalolin da mu ke fama dasu sai dai su ci gaba ta yadda za su kai ga tsayawar kome cik. Dabara dai ta rage tamu kodai muyi abinda ya kamata domin ceto da gyaran kasar mu ko kuma mu ci gaba da rayuwa cikin tsoro da rashin tabbas kamar yadda mu ke yi a yanzu.
Wannan ra’ayi ne wanda Ado Umar Lalu da Shamsu Mohammed Funtu suka rubuto

Awesome
  • User Ratings (0 Votes) 0
Share.

About Author

Leave A Reply