NIMASA Da NLNG Sun Kafa Kwamiti Don Inganta Ayyukan Su

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Abubakar Sadiq
Majalisar gudanarwa ta hukumar kula da iyakokin ruwa na kasa-NIMASA da ta kamfanin sarrafa iskar gas ta kasa-NLNG sun amince da kafa kwamiti da zasu yi aiki tare don cigaban kasa.
A wata sanarwa da mataimakin darakata a sashin hulda da jama’a na hukumar kula da iyakokin ruwa na kasa Mr Osagie Edward ya rabawa manema labarai, ya ce an cimma matsayar ne a lokacin da shugaban kamfanin na NLNG, Dr Philip Mshelbilia ya ziyarci hukumar NIMASA.
Dr Philip Mshelbilia yayi bayanin cewa hukumar NLNG ta dukufa wajen daukan ma’aikata ‘yan kasa, yana mai nuni da cewa a shirye suke su hada hannu da NIMASA wajen inganta tsaron dukiyoyin kasa a kan iyakokin ruwa. Ya lura da cewa kamar NIMASA, kamfanin NLNG ta baiwa horas da ma’aikatan ta muhimmanci don suyi fice a harkokin ayyukan kula da iyakokin ruwa a duniya.
Ya kara da cewa a kokarin da kamfanin ke yi na cimma muradunta, ta ga ya dace ta hada hannu da NIMASA da sauran masu ruwa da tsaki don ciyar da kasar nan gaba.
Dr Philip Mshelbilia ya kuma yabawa hukumar ta NIMASA dangane da ayyukan da take gudanarwa a tafkin guinea inda ya bayyana shi a matsayin gagarumar nasara a yaki da ayyukan bata gari a tafkin.
A nashi tsokacin, Shugaban hukumar ta NIMASA, Dr Bashir Jamoh ya lura da cewa hadin gwiwa tsakanin NIMASA da kamfanin NLNG zai yi matuqar inganta ayyuka a bangaren iyakokin ruwan kasar nan. Ya bada tabbacin cewa hukumar ta NIMASA a shirye take don yin aiki tare da kamfanin NLNG.
Da yake yabawa NLNG wajen samar da kyakkyawar yanayin horas da matuqa jirgin ruwa kuwa, Shugaban hukumar ta NIMASA yace a shirye hukumar take don yin gogayya da sauran takwarorin ta na duniya.
Ya kara cewa da hukumar na aiki tuquru wajen ganin cewa ta bada shaidar ingantaccen horaswa daidai da na zamani don kamfanin NLNG ta samu sauqin amincewa da wadanda NIMASA ta horas.

Share.

About Author

Leave A Reply