NSCDC Ta Tura Jami’anta 200 Don Lura Da Zaven Cike-Grubi A Jigawa

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Hukumar NSCDC ta bayyana cewa, ta samar da jama’ai 200 don lura da yadda za a gudanar da zaben cike gurbi a ranar Asabar 6 ga watan na mazabar Kafinhausa a jihar JIgawa.

Jami’in watsa labarai na hukumar, Mr Adamu Shehu, ya sanar da aka a tattaunawarsa da manema labarai a garin Dutse ranar Juma’a, ya ce, rundunar za ta ba kayan zabe dukkna tsaron da ya kamata.

Ya kuma kara bayanin cewa, za a tura jami’an ne don lura da mazabu 6 da akwatuna 118 don tabbatar da an yi zabe lafiya ba tare da wani matsala ba.

Ya kuma jami’an hukumar za su hada mai ne sauran jami’an tsaro don samun nasarar da ake bukata na gudanar da sahihin zabe.

A ranar Asabar be za a gudanar da zaben cike gurbin bayan rasuwar dan majalisa Adamu Baban-Bare, mai wakilatar mazabar Kafinhausa.

 

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply