NSCDC Za Ta Yi Amfani Da Kimiyya Da Fasaha Wajen Yaki Da Ta’addanci—Shugaban Hukumar

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Hukumar NSCDC a sanar da cewa, za ta fara amfani da fasahar kimiyyar wajen yaki da ayyukan ta’addanci da ake tafkawa a halin yanzu a fadin kasar nan, za kuma ta fara ne da tsarin nan na ‘Integrated Electronic Arrest Reporting System (I-EARS)’, wajen tattara bayanai akan ayyukan ta’addanci da ke tafkawa a fadin kasar nan.

Shugaban rundunar, Mr Ahmed Audi, ya bayyana haka a takardar da jami’in watsa labaransa, Mr Olusola Odumosu, ya sanya wa hannun aka kuma raba wa manema labarai a garin Abuja ranar Laraba.

Ya ce, tsarin na I-EARS zai taimaka wajen tattara bayanai akan abubuwan da suka shafi masu aikata laifukka da nufin samar da tsarin da za a fuskancesu gaba daya.

Shugaban hukumar ya kuma umarci dakarunsa su tsaurara matakan tsaro a dukk inda suke aiki don tabbatar da tsaro a fadin kasar nan a daidai lokacin da ake gudanar da buukuwan sallah.

 

Share.

About Author

Leave A Reply