NYSC Ta Kaddamar Da Gangamin Tsafface Muhalli A Kano

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A ranar Asabar ne hukumar NYSC ta kaddamar da shirin tsaftace mullali na shekarar 2021 a dukkan kananan hukumomin jihar Kano gaba daya.

Da yake kaddamar da shirin a garin Kano, Shugaban hukumar Brig.-Gen Shuaibu Ibrahim, ya ce, an shiriya gangamin ne a fadin duniya a matsayin mataki na farko don kare al’umma daga kamuwa da cututttuka.

Shugaban hukumar wanda ya samu wakilcin shugabar hukuma a jihar, Hajiya Aisha Tata-Muhammad.

Ta ce, dole a kara kaimi wajen fadakar da al’umma bukatar tsaftace muhalli tare da kuma kula da tsaftar jiki gaba daya don kare kai daga cututtuka.

Ta kuma kara da cewa, za a nemi dukkan jama’a su shiga shirin don a hada hannu tare da kuma sanya ido akan kare barkewar cuta a fadin jihar.

Tunda farko wani shugaban al’umma, Malam Bala Dabo, ya yaba wa shirin ya kuma bukaci al’umma su bayar da nasu gudummawar don a samu nasarar da ya dace.

Share.

About Author

Leave A Reply