Osinbajo Ya Tattauna Da ‘Yan APC Masu Fada A Ji A Shafukan Sada Zumunta

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Mataimakin  Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce Gwamnatin Tarayya a shirye ta ke waje tallafa wa matasa don amincewa da kudurin haramta kalaman batanci da ke gaban Majalisar dokoki.

Osinbajo ya bada tabbacin hakan ne ranar Litinin a Abuja

Mataimakin Shugaban kasan ya bada tabbacin cewa gwamnati ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen yin ayyukan da suka shafi matasa ba, musamman kafafen sadarwan da za su amfanar da al’umma.

Shi ma da ya ke jawabi a zaman da aka yi ta yanar gizo, Alhaji Ahmed Ismaeel, Shugaban matasan APC ya bayyana zaman a matsayin irinsa na farko a Nijeriya, inda ya ce jam’iyyar za ta ci gaba da shirya irin zaman daga lokaci bayan lokaci.

Ya ce masu kare jam’iyyar a yanar gizo da masu fada a ji ne suka shirya taron.

Alhaji Ahmed Ismaeel ya ce duk dai jam’iyyar ta rasa zaben jihar Edo, za ta yi bakin kokarinta wajen ganin ta lashe na Ondo da za a yi ranar 10 ga watan Oktoba.

Rahotanni sun nuna cewa kusan matasan APC masu fada a ji 100 ne suka halarci zaman.

 

Share.

About Author

Leave A Reply