PDP Bangaren Kwankwansiya Ta Jaddada Shirinta Na Kauracewa Zaben Kananan Hukumomin Jihar Kano

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Bangaren Kawankwasiyya na jam’iyyar PDP ta kara jaddada kudurinta na janyewa tare da kauwacewa zaben kananan hukumomi da aka shirya gabatar wa a fadin jihar Kano a ranar 16 ga watan Janairu 2021.

Shugaban bangaren, Alhaji Shehu Sagagi, ya bayyana haka a yayin da yake tattauanwa da manema labarai a garin Kano ranar Laraba.

Bayani ya nuna cewa, hukumar zabe ta ayyana jam’iyyar a cikin jam’iyyar siyasar da za su shiga zaben da za a gabatar a ranar Asabar.

Amma Sagagi ya bayyana cewa, tuni jam’iyyar ta maka hukumar zaben a gaban kotu akan sanar da cewa za ta shiga zaben don kuwa tun kotu ta haramta daya bangaren a mastayin jam’iyyar siyasa.

“Shugaban hukumar yana nuna kamar dai ya jahilci doka ko kuma bana abubuwa kamar wani dan siyasa.

“Mun bayyana cewa ba za mu shiga zaben ba kuma tuni muka yi nasara a kan haka a babbar kotu.

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply