Ra’ayi: Gwamnatin Katsina Da Fada Da Mace

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Safiyanu Abdullahi Safana

Katsinawa mun yi suna a ciki da wajen kasar nan a fannonin rayuwa masu yawa. Amma duk Bakatsinen asali yana tunkaho da wata karin magana da ke cewa “Katsinawa kunya gare ku ba dai tsoro ba”.

Wannan karin magana tana nuna halin girma da karramawa da Katsinawa ke da shi a hannu guda wanda ya sa ake yi wa Katsina kirari “ta Dikko dakin kara” a dayan hannun kuwa Katsinawa mutane ne wadanda basa shakka wajen fadin gaskiya a kan kowane ne indai abu ne da zai kai ga samin mafuta a al’amari.

Jihar Katsina tana sahun farko na jihohin kasar nan da suke da tsaro da kuma zaman lumana.
Sai dai wannan yanayi na zaman lafiya da lumana a Jihar Katsina ya shiga wani mawuyacin hali sakamakon ayyukan barayin shanu, maharan daji da masu garkuwa da mutane domin kabar kudin fansa. Wadannan ayyuka na yan-ta’adda sun sanya zaman lafiya ya tabarbare a inda yanzu Katsina ta zama a sahun gaba na jihohi mafi hadari musamman wasu kananan hukumomi da suka zama sun koma kamar wurin da babu gwamnati domin yan-ta’adda suna yadda suka ga dama suna cin karen su babu babbaka.

Wannan tabarbarewar tsaro ta yi sanadiyyar rasa rayuka, jikkata al’umma, sacewa da salwantar dukiya mai dinbin yawa tare da tilastawa mazauna kauyukan da abin ya fi shafa gudun hijira zuwa wasu gurare domin tsira da rayuwar su.

A kokarin kawo karshen wannan aika aika gwamnatin Katsina tayi kokarin sasanci dayin afuwa ga yan-ta’addan da suka aje makaman su suka rungumi sulhu wanda aka nuna mai-girma Gwamna Aminu Bello Masari ya halarta aka nuna a gidan talabijin, kuma gidajen radio da jaridu suka kawo rahoton.

Sai dai wannan a sulhu kwalliya bata biya kudin sabulu ba saboda har yanzu ana cigaba da satar mutane, kashewa da kuma jikkata su.

Ba tare da wani inkari ba hakkin gwamnati ne kare rayuka, mutunci da dukiyoyin al’ummar da suke mulka. Sakamakon yawan kashe kashen jama’a Mai-Girma Gwamna da kan shi ya bayyanawa duniya gwamnatin shi ta gaza wajen tsare rayuka da dukiyar Katsinawa da samar da tsaro a dukkan fadin Jihar bama kamar yankunan kananan hukumomin da suka fi mafi hadari.

Abin da ya dace ga kowace gwamnati tayi idan aka sami taka doka da masu aikata laifukan tarzoma shi ne ta dauki matakin babu sani babu sabo a tabbatar da anyiwa wadanda aka jikkata da sauran al’umma adalci domin kawo karshen ayyukan tarzoma a Jaha.

A duk inda aka sami yaduwar ayyukan tarzoma gwamnati kan tashi tsaye ta zage dantse domin ta tallafawa wadanda abun ya shafa a sake tsugunar dasu tare da sama masu tsaro kamar yadda muke ganin Mai-Girma Gwamnan Borno Prof Umara Zulum yakeyi ba dare ba rana ganin ya taimaka masu wanda yayi sanadiyyar tsallake rijiya da baya saboda maharan boko-haram suna yiwa tawagar sa kwanton bauna da yayi sanadiyyar rasa rayukan jami’an tsaron da ke bawa gwamna da tawagar sa kariya.
Sai dai wani abu da ya daurewa mutane kai shi ne maimakon gwamnati tazo da cikakken tsari na taimakon wadanda aka jikkata sai gashi tazo da wasu tsare tsare da aka bayyanawa jama’a daga bakin Mai-Girma Sakataren Gwamnatin Jaha Dr Mustapha Inuwa tsarin sake tsugunar da maharan daji da masu garkuwa da jama’a wajen yi masu tanadin abubuwan more rayuwa kamar su makarantu, asibitoci da dai sauran su.
Sanar da wannan shiri ya nuna a fili halin ko in kula na gwamnati mai ci akan tausayawa wadanda aka jikkata ta karkata akalar ta wajen kyautawa yan-ta’adda.
Wannan tsari ko shirin gwamnati ya fusata al’umma, shin abun tambaya rashin sanin makamar aiki ce ko kuma wata boyayyiyar manuface ta cimma wasu gurika ko muradun kai na jam’ian gwamnati.
Hakan ne yasa Hajiya Bilki Kaikai a hirar da tayi da yan-jaridu ta nuna rashin jin dadin ta da kuma rashin dacewar wannan shiri da gwamnatin Katsina ta bullo da shi a daidai lokacin da yangudun hijira da maharan daji suka tagayyara suke cikin halin ni yasu.
Maimakon gwamnati tayi nazari da idon basira da yin hangen nesa a sake shawara, sai ta buge gurfanar da ita a gaban sharia tana tuhumar ta da aikata ba daidai ba a lokacin da take kan aiki.
Sai dai abun tambaya a nan shi ne tuntuni gwamnati bata tashi gurfanar da ita a gaban sharia sai da ta caccaki wannan shiri na gwamnati gani cewa mata da kananan yara da aka kashe mazajen su, yaya da yan-uwan suna cikin halin kunci rayuwa?
Mu a tunanin mu shi ne gwamnatin Katsina zata mayar da hankalin ta wajen mayar da gamsassshiyar amsa akan duk zargin da Mai-Kwarmaton nan Mahadi Shehu yake bayyanawa duniya yadda ake watandar kudi a Katsina sai aka bige da fada da mace maimakon fada da Mahadi.
Muna kira da Mai-Girma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya umarci hukumomin EFCC, ICPC da NFIU da su gaggauta gunanar da binciken kwakwaf akan yadda gwamnati mai ci take kashe kudin jahar domin yiwa yanjaha cikakkun bayanan yadda ta kashe kudin jahar.

Safiyanu Abdullahi Safana ya rubuto ne daga Jihar Katsina

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply