Ra’ayi: Kalubalen Matasan Arewa

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Matasa sune abin babban alfahari ga kowace al’umma a fadin duniya. Matasa sune ke kan gaba wajen yin aiki tukuru domin samawa al’ummarsu kyakyawar makoma da zata kawo ci gaba mai dorewa.
Wannan ne ya sa ake ma matasa lakabi da shugabannin gobe, domin ana sa rai sune za su maye guraben iyaye da kakanni idan sun shude su cigaba da tafiyar da harkokin su akan tsare-tsare da kuma kyawawan manufofi.
Rike ragamar jagorancin al’umma tana samuwa ne idan matasa sun sami horo da kwarewa sosai a fannonin rayuwa daban-daban masu muhimmaci.
Sai dai idan muka yi duba ta tsanaki za mu ga matasanmu na arewacin Nijeriya an yi mana nisa fintinkau wajen sanya kishin al’ummar su a dukkan bangarori da fannonin rayuwa.
Yankin arewacin Nijeriya yana fama da matsaloli iri iri da suka zamewa yankin alkakai da yi masa tarnakin da kawo cikas ga cigaban yankin da al’ummar yankin baki. Wadannan sun hada da rashin ayyukan yi da ke haifar da zaman kashe wando ga dimbin matasan, talauci, koma bayan harkar ilimi, matsalolin tsaro, matsalolin tattalin arziki, kiwon lafia da dai sauran abubuwan kyautata rayuwar al’umma.
Babban abin da ya kamata Matasan Arewacin Nijeriya su saka a gaba shi ne matakan da ya kamata a dauka domin magance wadannan matsaloli.
Sai dai maimakon haka Matasan Arewa yanzu sun fi mayar da hankalinsu wajen kare muradun iyayegidan su fiye da muradun jama’a ta yadda ake anfani da su wajen cimma burin siyasa ko wasu boyayyun manufofi.
Tabbas babu mahalukin da zai ce yana farin cikin tabarbarewar harkokin tsaro a Arewacin Nijeriya da ma dai kasar baki daya.
A ci gaba da muzgunawa ‘yan Arewacin Nijeriya, Gwamnan Jahar Ondo ya bai wa Fulani Makiyaya wa’adi na su fice daga Jahar cikin sati daya wanda yin hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin Nijeriya. Amma abin mamaki sai ga shi babu wata kungiya ta Matasan Arewacin Nijeriya da ta fito fili ta kalubalance shi.
Wannan wa’adin da Gwamna Jahar Ondo ya bai wa Fulani Makiyaya wani zakaran gwajin dafi ne ta yadda za a kara tsangwamar ‘yan Arewa a jahohin kudancin kasar nan wanda da yayi nasara sauran zasu biyo baya.
Da sannu sannu an ragargaza Arewacin Nijeriya ta hanyar rikice rikice da suka addabi yankin kama daga na kabilanci, addini da kuma aikata miyagun laifuka. A cikin shekaru kusan shadaya da suka wuce rikicin boko-haram da matsalolin barayin daji masu garkuwa da mutane sunyi sanadiyyar rasa rayukan dubban mutanen , dukiya ta biliyoyin kudi, raba mutane da gidajen su da garuruwan su suka zama yangudun hijira a kasar su, raguwar noma da kiwo da suka zama tushen arzikin mu tare da tabarbarewar harkokin kasuwa da tattalin arzikin mu baki daya, ga kuma tabarbarewar tsaro da jefa al’ummar arewa cikin zaman tsoro da rashi tabbas. Wayannan matsaloli sun haifar da koma baya a dukkan fanonin rayuwar da kuma kyama daga abokan zaman mu na kudu inda suke ganin duk wani musulmi na arewacin kasar nan dan ta’adda ko barawon daji.
A irin wannan yanayi ya zama dole ku zage dantse da tashi tsaye haikan na ganin an matsawa gwamnati da masu fada aji kama daga Sarakuna, Yankasuwa, Yanboko da Malaman addina lamba su tashi tsaye haikan suyi kira da babbar murya domin kwatowa mutanen mu yancin su kamar yadda aka debawa inyamurai wa’adi subar arewa bayan sun bayar da irin wannan sanarwa.
Ku sani fa abinda ya ci Doma ba zai bar Awe ba, idan har tsangwamar da akewayiwa Fulani tayi tasiri sakamakon wasu bara gurbin cikin su da suka zama barayin daji to babu shakka kowa sai ta shafe shi.
Ya dai dace ga Shugabanni Matasan Arewacin Nijeriya masu ina da zanga zanga su sake dabaru ta yadda za a rinka jin duriyar su akai akai ba su zama ana amfani dasu bane kawai akan cimma muradun siyasa ba tunda Arewa ta zama matattarar matsaloli.
Baya ga wannan ya kamata jagororin Matasan Arewacin Nijeriya su mayar da hankalinsu wajen kira da masu ruwa da tsaki a yankin da su sake salon tafiya ta yadda za’a dora arewa kan manifofi da za su amfani yankin da al’ummar yankin baki daya.
Kwanannan aka yi zanga-zangar ENDSARS wadda ta yi sanadiyyar rasa dukiyoyi da rayukan ‘yan Arewa da ke zaune a kudancin kasar nan da masu zuwa fatauci, amma shiru ba mu ji duriyarku ba a kan a biya su diyya.
Idan za a fuskanci gaskiya da tunkarar wadannan matsaloli tun kafin a gama daidaita Arewa gaba daya to sai mu farka baki daya ko kuma mu ci gaba da rayuwar kaskanci.

Daga Ado Umar Lalu, 
Shamsu Mohammed Funtua,
Lawal Sani Usman, da
Lawal Saminu

Share.

About Author

Leave A Reply