Ra’isi Ya Zama Shugaban Kasar Iran Na Takwas

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Umar Shuaibu

Sayyid Ibrahim Ra’isi ya lashe zaben Shugaban kasar Iran da aka gabatar jiya Juma’a 18 ga watan Yuni, 2021.

Wannan shine karo na 13 da ake gabatar da zabe a kasar tun bayan juyin juya halin da al’ummar kasar suka gabatar karkashin jagorancin Ayatullahi Khomeini. Inda Ra’isi kuma ya zama shugaban kasa na 8.

Kafin lashe zaben na shi, Ra’isi ya taba zama shugaban haramin Imam Ridha, Limamin Shi’a na 8 dake Mashhad a kasar ta Iran na tsawon shekaru, daga bisani kuma ya rike shugabancin ma’aikatar shari’a na kasar.

Tuni Shugaban kasa mai barin gado Hasan Rohani yayi tattaki zuwa ma’aikatar shari’a domin taya sabon shugaban kasar murnar lashe zaben da yayi.

Share.

About Author

Leave A Reply