Rashin Daukar Mataki Mai Tsauri Ya Sa Har Yanzu A Ke Ci Gaba Da Yi Wa Yara Fyade —Dakta Bashir Abdullahi

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Mai karatu wannan itace cikakkiyar tattaunawar da wakilinmu Yahaya M Abdullahi ya yi da daya daga cikin Malamai a babban jami’an jihar Nasarawa dake Keffi, wato Dakta Idris Bashir Abdullahi daga Jami’ar Nasarawa kuma daya daga cikin masu fashin baqi na yau da kullum kan al’amarin siyasa da karatu a jihar Nasarawa, anyi wannan tattunawar ne bayan kammala jawabin da Dakta yayi a dakin taro na Jami’ar bayan gudanar da gagarumin taro akan hakkin yara kanana da ake musu fyade a fadin jihar Nasarawa dama kasa baki daya. Asha karatu lafiya.
Yanzu ana lokaci ne na take hakkin Yara mata ta hanyar yi musu Fyade, ko Ya ya Dakta yake kallin wannan lamarin?
Dakta: Harkar Fyade wani abu ne wanda Malamai a makaranta da sauran manyan mutane a Kasa sun yi rubutu akan Fyade, wato shi Fyade abu ne da a ke yi na karfi kuma ba sai ga mace ba, a yanzu har Namiji ana masa Fyade amma abin da muke so mutane su gane shi ne, Fyaden da ake yi yanzu ya canza kamanni ya zama wani abu daban, yanzu manya ne ke yi da kananun yara, Yara ‘yan wata biyu a duniya ko kuma yan shekara uku a duniya za ka ga an musu Fyade, to wannan magana na Fyade dole mu zauna mu duba mu gani cewa, shin menene salsalar da ya sa ake aikata wannan aika-aikar na Fyade?
Wasu sun ce halin kulle ne da ake ciki wato ‘lockdown’ alhalin ba shi bane, in rashin aiki ne zai sa kayi Fyade ai lokacin da ake aiki nan ma ana fyade, abin da za mu yi la’ari dashi shi ne, mu duba abubuwa makamancin haka, wadand suka yi rubutu suna cewa abin da kesa fyade shi ne wanda ake musu fyade in ya zamanto ba a kula dasu misali Namiji yaga yarinya karama kyakkaywa tana tafiya a cikin yanayi mai kyau tana ta yawo a unguwa kaga wannan zai iya mata fyade saboda ya ganta a waje ba kula, amma idan tana cikin gida fa ya kamata mu duba wannan lamarin nan ma mu dinga killace yaranmu a gida kada mu dinga barinsu suna yawo ba tare da mun san ina suke zuwa ba.
Na biyu kuma abin da yake firgitar damu a wannan lokacin in ka duba kaga irin ‘kananan yaran da ake ma fyade, abin da za ka tambaya shin wadanda suke aikata wannan aikin na fyade shin basu da hankali ne ko kuma wani ciwone na hauka yake so ya kama su, abin da za mu duba mu gani, Ni a nawa tunanin, yanzu abun ya zama na hauka domin kuwa ya kamata mu dinga duba abubuwa biyu na farko shi ne wanda na fada maka cewar rashin kulawa da yaran da ake musu wannan aikin, har yanzu Hukumomi basu hukunta wadanda aka kama su da wannan laifin ba, shi ya sa wanda zai yi wannan aikin zai duba ai ba a hukunta wanda yayi na baya ba ko kuma ai da na yi a baya ma ba a min wani hukunci ba saboda tumda babu wani hukunci to nima zanyi naji ko kuma zan sake aikatawa in ya zamanto mai aikatawan ne, amma abin da muke so ayi la’akari dashi a nan shi ne, abu ne da ya kamata ace ba wai kawai hukuma be zata yi ba kowa yana da rawar da zai taka a wannan lokacin tun daga Dan Sanda har kan Gwamna, ya kamata a zauna a duba idan ma za a yi doka ma masu aikata wannan mummunan aika-aikar ya kamata dokar ya zamanto tsakaninmu ne daga cikinmu, akwai wani Malami yana karantar da bangaren Shari’a ya ce in za ka yi magana akan hukunci za ka yi ne da yanayin jama’ar da kake tare dasu, in kayi dokar da bai shafi mutanen wajen ba ba zai yi tasiri ba, kamar yanzu misali ka dauki dokar Keffi kayi aiki dashi a Kano ba zai yi aiki ba, sai dai kayi dokar Keffi da Keffi kawai to ya kamata a duba wannan maganan na fyade, iyaye su fada ma yaransu ga matsalolin dake faruwa, wannan lamarin ya wuce maganan mutum yayi domin ya ji dadi magana ne na wani abu daban wanda ba wanda ya sani sai wanda ya aikata hakan.
Ko akwai wani Shawarar da Dakta zai bama Gwamnati kan masu aikata wannan aika-aikar?
Shawarana ga Hukuma idan an kama masu irin wannan mummunan aika-aikar, kafin ma a zauna ace an kaddamar da wannan dokar, Ni shawarar da zan bayar shi ne kawai a yanke masa mazaqutarsa in dai in aka yanke zai rayu to kawai a yanke masa din, idan kuma ba zai rayu ba to a kashe shi kawai shi ne babban abin da za’ayi domin magaanin wannan mummunan aika-aikar, daga lokacin da aka kama shi ana kai shi to kawai a aikata masa wannan aikin na hukunci ko a kashe shi, ko kuma a yanke masa Mazaqutarsa kawai, kada ma a saka masa Bindiga, ayi amfani da bangaren rataya a rataye shi, a fito dashi kuma a fili gaban jama’a kowa na ganin irin hukuncin da ake yanke masa komai kudinsa kuwa, komai iyalensa, in ka duba sauran kasashen duniya za ka ga duniyar mutum bai hana ayi masa hukunci akan abin da ya aikata misali amerika duk duniyar mutum in dai yayi laifi to za su hukunta shi dai-dai da laifinsa, amma a Kasarmu ta Nijeriya babu doka, ya kamata Gwamnati ta yi la’akari da dukkan Jami’ai tun daga Dan sanda har Hukumomi da ministoci kada fa wannan sakacin ya sa mutane su fara daukar doka a hanunsu, kamar Ni misali na yi karatun boko sosai, amma fa idan ka taba min yarinya fa bama doka, zan manta da doka ne kawai, Ni da kai na zan dauki doka a hannuna matukar za ka tana min yarinya da sunan za ka aikata fyade da ita ko ka aikata.

Share.

About Author

Leave A Reply