Rashin Tsarin Tafiya Kan Manufa Ne Ya Janyowa Arewa Matsaloli, Daga Ado Umar Lalu

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +
Duk al’ummar da ke son ta ci gaba sai ta yi wa kanta tsari na manufofin da za su saka a gaba domin kyautata rayuwar al’umma.

Idan akwai matsaloli ko kuma karancin su, akan yi tsari na gajeren zango saboda a yi wa jama’a maganin manya da kananan matsalolin dake hana masu walwala. Wannan shi ne abin da zai sakawa talakawa nutsuwa kan cewa gwamnati da masu fada aji sun kula da halin da suke ciki.
Bayan wannan sai a dauki tsari na matsakaicin zango domin a ga nasarorin da aka samu a matakin gajeren zango da kuma matsalolin da aka samu a kokarin samar da kayan inganta rayuwa a kara zage dantse da azama.
Bayan wannan shi ne samun tsari na dogon zango da zai dace da kowane irin zamani domin ganin ba a bar al’umma a baya  ba.
Kafin zuwan turawa da bayan zuwan su arewacin Nijeriya ta kasance yankin da take da cikakken tsari na tafiyar da al’amurran jama’a a dukkan bangarorin rayuwa da ya zama abin alfaharin mu da ya bai wa turawan mulkin mallaka sha’awa. Wannan tsari ya ci gaba da gudana har lokacin da aka samu mulkin kai arewacin Nigeria ya zama tauraro da zakara wajen bayar da gudunmuwa mafi tsoka ta fanni tattalin arzikin kasa saboda kulawa da noma da kiwo wayanda sune tushen arziki.
Baya ga haka shugabannin mu na arewa sun zama masu gaskiya, rikon amana da kuma son talakawan su. Bugu da kari Sir Abubakar Tafawa Balewa, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto da sauran su basu da zarmewa da son tara abun duniya shi yasa suka tsayu akan yiwa talakawan su hidima saboda inganta rayuwar su kamar sama masu guraben aiki, daukan nauyin karatun yayan talakawa  kyauta a ciki da wajen Nigeria, da tsare masu rayuka da dukiyoyin su.
Dr Mamman Shata a lokacin da yaga abubuwa sun fara ja baya yayiwa yan arewa hannun ka mai sanda a wakar sa idan yake cewa “mu tashi mu farka yan arewa musan bacci aikin kawai ne”. Baccin kwalwar da manya arewa sukayi shine sakin harkar noma saboda samuwar man fetur musamman shugabanin da suka maye guraben da Sir Abubakar Tafawa Balewa da Sir Ahmadu Bello suka bari domin dorawa akan inda suka tsaya.
Sai dai abun takaici, shi ne bayan kashe shugabanin mu masu son talakawa da ci gaban su kwatsam sai abubuwa suka fara canzawa inda wayanda suka maye gurbin su sai suka mayar da hankalinsu akan son kai maimako san al’umma, gina kai maimakon gina al’umma, zarmewa maimakon hakuri da kadan, cin amana ya maye riko da gaskiya, gina manyan gidaje maimakon manya asibitoci da makarantu dadai sauran su.
Idan muka dubi sauran yankunan Nigeria wayanda suka hada da kudu maso yamma, kudu maso gabas da kudu maso kudu dukkaninsu suna tafiya akan manufofin da dazasu ciyar da yankunan su da al’ummar su gaba kuma suna dagewa akan matsayin da suka dauka kuma suje duk inda ake zuwa domin muradun yankin su.
Duk lokacin da wani abu ya bujiro masu suna ajiye banbancin siyasa, akida, ubangida da addini domin kaiwa ga cimma gurin da suka saka a gaba.
Bugu da kari, duk gazawar nasu sukan tsayu a kan sa su goya masa baya domin kada ya kunyata, kuma basa bari matasan su, su ginu da harkar cin zarafin junan su ba duk yadda za’ayi akwai biyayya da girmama juna.
Bayan haka mutanen kudu basu yarda da suyiwa dan-uwan su zagon kasa ba a duk matsayin da ya taka a gwamnatance ko ta hanyar kasuwa suna zama ne su kara taimakawa su gina juna ba su rusa junan su ba. Samsam basa yarda da mummunan  al’adar da tayi katutu a cikin mu ta a fasa kowa ya rasa sai dai a yada kowa ya samu yadda za’a samu yalwa da yaduwar arziki a tsakanin su.
A duk lokacin da yankudancin kasar nan suka sami kowace irin dama ko daukaka babban abunda zasuyi kokari suyi shine a duk lokacin da suka zo irin ganawar da suke ta karshen shekara  basa alfahari da irin manyan motocin da suka zo dasu, manyan gidajen da suka gina, yawan tafiye tafiyen su zuwa kasashen wajen ko irin tarin kudin da suka mallaka ba. Koda yaushe abun alfaharin su shine irin gudunmuwar da suka bayar a shakarar da ta gabata wajen cigaban yankin su da kuma al’ummar su kama daga gina makarantu, samar da ruwan sha, gina hanyoyi, daukar nauyin karatun talakawa,  basu jari, sama masu guraben aiki da sauran su.
Idan muka dawo arewa zamuga cewa muna zaman kara zube ne bama tunanin wace irin gudunmuwa zamu bayar domin cigaban yankin mu da kuma al’ummar mu sai yankadan daga cikin mu. A duk lokacin da kaga manyan mu daidai kun su ko a kungiyance sun tashi haikan suna tada jijiyoyin wuya da ka zakaga a zahiri sunayi ne domin maslahar su ta siyasa, tattalin arzikin su ko kuma iyalansu, amma basa damuwa da maslahar talakawa kamar yadda Sir Abubakar Tafawa da Sir Ahmadu Bello sukayi.
A kwananan munga yadda mutane yakin kudu maso yamma sukayi namijin kokari domin tunkarar matsalolin tsaro a jahohin su, suka kafa Amotekun wanda babu inda basu je ba, kuma babu wanda basu gani ba domin suga an kafa wannan hukumar tsaron tasu bata hadu da cikas ba. Sanin kowa ne gwamnatin tarayya ta nuna adawar ta akan wannan hukuma amma dole haka aka hakura aka kyale su saboda sun dunkule wuri daya dayin magana da aiki tare.
Amma abun takaici kamar yadda na fada a baya arewa bamu da jagorori da zasu sa al’umma a gaba su nuna masu kauna da ajiye duk wani banbancin ra’ayi saboda maslahar jama’a sai dai saboda biyan bukatar kan su da ta iyalansu.
Anshayin tarurruka babu adadi domin samo bakin zaren  matsalolin arewa, amma suna tsayawa ne a sanarwar bayan taro wanda shi yasa arewa ta daidaice sakamakon zaman yanmarina idan rashin aiki, talauci, matsalolin tsaro, rigingimu da sauran matsalolin da suka zame mana tarnaki wajen samun cigaba mai dorewa. Manyan mu suna amfani da talakawa domin biyan bukatun su amma basa iya biyawa talakawa nasu bukatun sai yankadan. Lokaci fa yayi da yakamata manyan su farka daga barci domin maido arewa akan tafarki ta hanyar kawo manufofin da zasu warware mana matsalolin da suka sha kan mu saboda inganta arewa da kyautata rayuwar yan-arewa kafin wuri ya kure.

Ado Umar Lalu
adoumarla57@gmail.com
Awesome
  • User Ratings (0 Votes) 0
Share.

About Author

Leave A Reply