Rashin Tsaro: Shugaba Buhari, Monguno Da Aikin Tattara Bayanan Sirri, Daga Gidado Ibrahim

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Tsaro shi ne abu na farko, mafi muhimmanci a wurin kowacce gwamnati, musamman a gwamnatin Dimokradiyya irin Nijeriya. Wannan ne ya nuna dalilin da ya sa Shugaba Buhari ya zage damtse wurin lalubo mukarrabai wadanda za su taimaka mishi wurin fuskantar matsalar tsaron Kasar.

Tattara Bayanan Sirri a harkar tsaro tamkar misalin numfashi ne ga dan Adam. Wannan ne ma ya sa Shugaba Buhari ya lalubo Janar Babagana Mongonu a matsayin Mai ba shugaban shawara kan harkar tsaro. Tun bayan shigarsa ofis, Mongonu ya ke aikin tattara bayanan sirri, bincike da kuma yin amfani da wadannan bayanai domin dakile matsalar tsaro.

Babagana Mongonu ya yi kokari matuka wurin hada kawunan bangarorin tsaro a wannan aikin. Wadanda suka hada da bangaren tattara bayanan sirri na soja, ‘yan sanda, da kuma na jami’an tsaron fararen kaya na ciki da wajen Nijeriya. Hatta hukumomin da ke kula da shigi da ficin kudin daukar nauyin ‘yan ta’adda sun samu tallafi sosai daga wannan nagartaccen jami’in tsaro, Janar Monguno.

A wurin Janar Monguno, babu makawa ya fi muhimmanta batun tattara bayanan sirri fiye da komi. Wannan shi ne babban abin da ya sa a gaba, kuma da wannan ne ya ke ta samun nasarorin da ake gani a kasa. Kusan gabadaya rayuwarsa a harkar tsaro ya tafiyar da ita, bisa la’akari da irin wuraren da ya yi aiki da kuma mukaman da ya rike.

Saboda matukar damuwar da ya yi da yanayin ayyukan ‘yan bindiga a Jihar Katsina, NSA Monguno ya jagoranci BAbban Sufeton ‘Yan Sanda, Muhammad Adamu, Daraktan DSS, Yusuf Magaji Bichi da Daraktan NIA, Ahmed Rufai Abubakar domin ki ziyarar gani da ido jihar. A wannan ziyarar ne, Janar Monguno ne ya jaddada musu bukatar wanzar da zaman lafiya a kauyukan da ke fuskantar wannan barazana. Tawagar ta yi ganawar sirri da gwamna Masari inda ta tabbatar mishi da cewa za a yi wa tufkar hanci ba da jimawa ba.

Alal misali, a Arewa maso Gabas, mun ga yadda sojoji suke ci gaba da ragargazar ‘yan ta’addan Boko Haram, musamman a wuraren da suka fi karfi, wato jihar Borno. Sojoji suna ci gaba da tarwatsa su a sansaninsu da ke dajin Sambisa. Kamar dai yadda Kakakin wannan tawaga ta sojoji, Manjo Janar John Enenche ya fadi ne, “Wannan nasarar da suke samu na tarwatsa sansanin ‘yan ta’adda ana cimmata ne sakamakon bayanan sirrin da ake tattarawa.

Wannan nasarar da sojoji ke ci gaba da samu kaitsaye ana iya jingina ta ga irin salo da kamun ludayin Janar Babagana Monguno. Domin kuwa ya zo ne da sabon salo daban da wanda aka saba da shi a Nijeriya.

Kasancewar monguno a matsayin mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, yanzu kusan ana iya cewa Buhari ya cika alkawurran da ya daukarwa ‘yan Nijeriya yayin da yake kamfen. Musamman batun dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya da ma sauran sassan Nijeriya. Wannan zaman lafiya da aka samu a wasu sassan da a baya suke cikin bala’I ya haifar da kwanciyar hankali a kasashen da suke makwaftaka da Nijeriya.

Dole mu zama masu fadin gaskiya. Babu wata tantama halin da ake ciki na tsaro a yau ba daya ba ne da 2014, lokacin da rayukan jama’a suka zama tamkar na kaji. Ba zamu manta ba, a wancan lokacin Kananan Hukumomi 17 da ke Borno suna karkashin Boko Haram ne. Duk sun dora tutocinsu.

Monguno, a matsayinsa na Mai ba shugaban Kasa Shawara daga shekarar 2015 zuwa yau, ya yi amfani da ofishinsa wurin kwato wadannan kananan hukumomi daga hannun ‘yan ta’adda. Ya kuma yi amfani da salo da dabarun yaki da Boko Haram har sai da ta kai ya cire zuluminsu daga zukatan ‘yan Nijeriya.

Wannan irin kwarewa ta aiki ta Janar Babagana Monguno ta nuna irin mutanen da Shugaba Buhari ya zabo kuma yake aiki da su. Kowacce gwamnati idan ta zo tana zuwa da tsarinta na tattara bayanan sirri, kuma da wannan tsarin ne aka amfani wurin fuskantar matsalolin tsaron da ke fuskantar Kasa.

Misali, Shugaba Buhari a watan Agustan shekarar da ta gabata ya bayar da umurnin cewa a karfafa alaka tsakanin sojoji da sauran bangarorin tsaro domin su rika tattauna bayanan sirri. Wannan kuma ya biyo bayan rahoton da Babagana Monguno ya ba shugaban Kasan ne na cewa ana samun yawon kananan makamai da alburusai a Nijeriya.

Domin dakile wannan yawo na kananan makamai din ne, ya sa Monguno ya bayar da shawarar a samar da cibiyar dakile yaduwar wadannan makamai a Nijeriya. An samar da cibiyar wacce take karkashin kulawar ofishin Mai ba shugaban kasa shawara. Yanzu ana ci gaba da bin matakan samarwa cibiyar matsuguni ne a dokar Nijeriya, sannan sai ta fara aiki.

A gabadaya rayuwarsa ta aiki, Janar babagana Monguno ya mayar da hankali ne wurin fahimtar yadda tattara bayanan sirri yake, da kuma yadda ake amfani da shi. Ya taimakawa hukumomi da dama wurin yin amfani da irin wadannan bayanai na sirri domin gudanar da ayyukansu.

A matsayinsa na lamba daya a harkar tsaron Nijeriya, Janar Monguno ya san kan aikinsa, ya kuma iya sajewa da duk wani yanayi da ya tsinci kansa domin yin mu’amala da mabambantan mutane. Yana yin komi a tsanake domin fahimtar wuraren da ke bukatar gyara da inda za a sauya.

– Ibrahim shi ne Daraktan Sadarwa da tsare-tsare na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa (PSC).

Share.

About Author

Leave A Reply