Rashin Tsaro: Umurnin Shugaba Buhari Da Gabatowar Nasara, Daga Gidado Ibrahim

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A tsarin gwamnati wanda aka dora shi bisa turbar dimokradiyya, shugaban kasa shi ne kwamandan askarawa. Ma’anar hakan na nufin shi ne shugaban tsaro na kasar, kuma shi ke daukar alhakin duk wani lamarin tsaron kasar. Wannan ne abin da Shugaba Buhari ya nuna da wannan umurnin da ya bayar ga shugabannin bangarorin tsari, inda ya ce su bankado ‘yan bindiga da masu garkuwan da suka addabi Jihar Katsina da ma sauran sassan Nijeriya.
Sabunta salon yaki da rashin tsaro a wannan bigiren ya haifar da fargaba da rashin tabbas a tsakankanin ‘yan Boko Haram da ‘yan ISWAP, ta yadda har shugabannin bangarorin tsaro za su iya bugun kirji a yanzu su ce an soma jin kamshin karshen Boko Haram a yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya da kuma ‘yan bindiga a Kudu maso Yamma.
A matsayinsa na Janar, Shugaba Buhari ya nuna cewa yana da kwarewar da zai iya kare Nijeriya da wanzuwarta. A yau, shugaban muguwar kungiyar nan ta Boko Haram, Abubakar Shekau da ‘yan ta’addansa sun firgice, suna cikin tsananin yunwa wanda hakan ya sa suka koma buge-buge wurin kai hari don samun abinci. Kwanan nan ma faifensa ya cika yanar gizo inda yake kuka yana neman a yi masa afuwa.
Ta wacce hanya ce shugaba ke gwada cancantarsa? Da farko dai duk wasu kayan aiki da bangarorin tsaro ke bukata an samar musu da su. Toh me zai hana su yin abin da ya dace? Matakin da Shugaba Buhari ya dauka shi ne duk wani nau’i na barna sai an kawo karshensa. Ya bada umurni wanda da shi sojoji za su fara wani atisaye wanda zai kawo karshen duk wani aikin ‘yan ta’adda a Jihar Katsina. Wannan abin a yi shewa da murna ne, domin zai daga darajar Nijeriya, kuma ya bayar da damar da masu sanya hannun jari za su shigo ba kakkautawa.
A ta bakin shugaban kasan; “Ana kan gudanar da wani babban motsi daga runduna ta musamman, wanda tsari da yanayinsa za a barshi a matsayin sirri, wanda lamari ne da zai kawo karshen duk wani barnan ‘yan bindiga da sansaninsu.
Domin ba wannan shiri goyon baya dari bisa dari, tuni rundunar farko ta fara sharar farge ga babban aikin da aka sanya a gaba.”
Shirin Shugaba na kawo karshen barayin Shanu, garkuwa da mutane da ta’asar ‘yan bindiga babbar nasara ce, wacce ke nufin babu gudu ba ja da baya har sai an kai ga nasara. Rashin tsaro da aka yi fama da shi a baya ya haifarwa da gwamnati da al’umma dimbin asarori, wanda hakan ke nufin gwamnatin da ta san abin da take yi ba za ta zuba ido tana kallo ba.
Mun gode Allah da wannan kokari na Shugaba Buhari na son dakile matsalar rashin tsaro, wanda kuma yake ci gaba da samun yabo daga shugabanni, masu ruwa da tsaki, da kungiyoyi. Ga shi nan yanzu an fara gani a kasa. Daga Borno zuwa Katsina, daga Neja zuwa Zamfara da Kaduna duk inda ka zagaya za ka ga ‘yan bindiga da masu garkuwa sun arce suna neman mafaka, saboda ganin yadda sojoji suke fatattakarsu. Bisa umurnin shugaban kasa, rundunar sojojin Nijeriya wani karsashi suke ji tamkar wadanda suka sha zumbur.
Wadannan nasarorin ba za a taba cimmu su ba tare da gudummawar shahararre, kwararren masanin harkar tsaro, mai ba shugaban Kasa shawara kan harkokin tsaro NSA, Manjo Janr Muhammed Monguno (ritaya), wanda kwarewarsa a harkar sanin tsaro ta kai intaha, wanda kuma shi ne ya sa yake da hangen nesa.
Kasantuwarsu shugaban sashen tsaro na Nijeriya a sama da shekara biyar, ana iya yin jinjinar ban girma da yabo ga wannan gwarzo. Daga lokutan da aka tsinci kai cikin zubar jinni, arangama tsakanin manoma da makiyaya duk sun zama tarihi, ‘yan Nijeriya sun koma rayuwarsu na yau da kullum. Wanda a baya ba a iya yin haka.
Tuni an koma rayuwa lafiya lau a jihohin da a baya suna cikin mugun hali. Manoma da Makiyaya da a baya basu ga maciji amma yanzu sun zama tamkar ‘yan uwan juna. Rikicin addini da kabilanci da suka addabi Jihar Filato duk a yanzu ba iska suka bi suka bace ba, a’a wannan duk ayyukan Janar Monguno ne.
Gari na karshe da Boko Haram ta kwace a Jihar Borno tuni an kwace shi, wanda tun ma kafin Janar Monguno ya shiga ofis. Tun bayan nan, gwamnati ta mayar da hankalinta kan sake ginawa da gyatta yankin na Arewa maso Gabas ta hanyar samar da Cibiyar ‘North East Development Commission’.
Kafin Janar Monguno ya shiga ofis a matsayinsa na NSA, an mayar da ofishin tamkar wani wurin wadaka da almundahana. Amma daga zuwan Janar Monguno sai ya haifar da al’adar bin ka’ida, bin diddigi wurin kiyaye amanar wadannan kudade. A matsayinsa na mutumin da aka haife shi ya taso cikin wadatar zuci, ba a taba samun Janar Monguno da laifin rashawa ko almundahana ba.
Janar Monguno mutum ne da idan ya fada, yake cikawa. Misali, lokacin da aka samu yanayin da ya haifar da dole a dage zaben da ya gabata, Janar Monguno ya yi alkawarin tabbatar da tsaro ga rayuka, da dukiyar al’umma. Kuma ya kiyaye wannan alkawai nashi. Masana sun tabbatar da cewa tun daga shekarar 1993 ba a taba samun zabe da aka gudanar cikin lumana irin na 2019 ba.
Yanzu ne babbar damar kawo karshen Boko Haram! Abin farin ciki ne ganin yadda tattalin arziki ke bunkasa tare da harkar tsaro. Harin da sojojin Nijeriya suka kai wa sansanin ‘yan boko haram a ‘yan kwanakin nan ya dagula musu lissafi da su da masu daukar nauyinsu. An dakile hanzarinsu na son mayar da Nijeriya kasashe irinsu Libiya da Siriya.
Muna iya ganin yadda gwamnatin Buhari ta mayar da hankali wurin tallafawa bangarorin tsaro da kayan aiki, ba kawai sojoji ba. Da umurnin Shugaban Kasa, wanda ya bayar bayan da ya kammala hada rahotannin sirri da shawarwarin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro NSA Monguno, nan ba da jimawa ba ‘yan Nijeriya za su shaida ganin karshen wannan annoba da ta fi shekara 10 tana addabar rayuwar mutanen yankin Arewa maso Gabas.
Masana da masu fashin baki sun tafi akan cewa, bisa yawan adadin ‘yan Boko Haram da aka kashe, karshen kungiyar da masu ingiza su daga waje wato ISWAP ya zo. Lokaci ne da ‘yan Nijeriya za su taimaka kudurin Shugaban Kasa na fatattakarsu.

Ibrahim shi ne Daraktan Sadarwa da tsare-tsare na kwamitin tallafawa Shugaban Kasa (Presidential Support Committee)

Awesome
  • User Ratings (0 Votes) 0
Share.

About Author

Leave A Reply