Rawar Da Rugage Ke Taka Wa Ga Barazanar Tsaro A Katsina: Ina Mafita?

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Tsarin zaman rugage wata al’adace da fulani makiyaya suke rayuwa akan ta tsawon zamani maitsawo da suka gada daga iyaye da kakanni.
Bisa wannan tsari fulani kan kafa bukkokin da rumbuna su a cikin gonakin na nan gida cen gida ta inda suke daure shanu da kananan dabbobin su a kusa da bukkokin su a cikin gona.
Fulani makiyaya mazauna ruga sukan shigo cikin gari da kasuwanni domin gabatar da harkokin su cikin zaman lumana, aminci, kyakkywar alaka da zumunci su da mutane mazauna gari.
Sai dai sakamakon bullar matsalolin satar shanu a Jahar Katsina da sauran makwabtan jahohi sannu a hankali sai rugage suka zama malaba ta barayin shanu wanda daga baya suka rikede zuwa satar mutane domin karbar kudin fansa.
Bullar wannan matsaloli ya sanya garuruwan da ke makwabtaka da rugage cikin zaman zullumi, firgici da barazanar tsaro iri iri da suka zama ruwan dare sakamakon dandazo da barayin daji sukayi a cikin rugage suna aikata laifuffuka da sukayi sanadiyar rasa daruruwan rayuka, dukiyoyi na daruruwan miliyoyi da tilastawa dubbai yin gudun hijira domin tsira da rayukan su.
Yadda maharan daji ke cin karen su babu babbaka a wasu kananan hukumomin wannan jaha ya sanya gwamnati mai ci tayi yunkurin sasanci da maharan daji inda suka cimma yarjejeniya ta dakatar da hare hare wanda har Mai-girma Gwamnan Katsina ya halarci bukin tuban maharan dajin.
Sai dai wannan yunkuri na gwamnati bai cimma nasara ba sai haihuwar da marar ido wanda ya kara jefa rayuwar Katsinawa cikin hadari na kisan gilla da satar dukiyoyin su da yiwa matan su fyade duk da dokar hana hawan babur da aka kafa wadda kusan tasirin ta ya tsaya ne a birane da inda wannan matsalar bata kai ba. Amma a malabar barayin na daji jamian tsaron basa iya tabbatar da bin wannan doka.
Zafafa wayannan hare hare ya sanya Katsinawa suka tashi haikan wajen kiraye kiraye ga gwamnati ta dauki kwakkwaran mataki ganin yadda lamarin barazana da matsalolin tsaro ke kara ta’azzara da tabarbarewa a Jahar.
Wayannan kiraye kiraye sun sanya gwamnatin tarayya ta turo da dakaru domin a dauki matakin babu sani babu sabo domin yin maganin yantaadda masu boyewa a rugage suna tada hankalin jamaar da basu ji ba basu gani ba.
Sai dai abun lura anan shine menene makomar wayannan rugagen da suka zama mafaka ga yantaada da suke amfani dasu wajen afkawa mutanen dake makwabtaka da dasu ko kuma matafiya masu wucewa akan hanya?
Shawara anan shine idan an kai ga nasarar kakkabe barayin daji daga cikin dazuzzukan Katsina ya zama wajibi gwamnati ta kawo karshen rugagen dake warwatse a kananan hukumomin da wannan bala’I ya shafa ta hanyar yanka masu filotai a hade su guri guda.
Wannan zai kawo karshen amfani da ruga da maharan daji keyi sukaiwa mutane hari. Idan muka lura a wasu sassan Katsina akwai garuruwan fulani da suke hade wuri guda suna gudanar da kiwon su a hannu guda babu tsangwama, a dayan hannu kuma suna gudanar da harkokin su tare da jama’ar gari cikin lumana.
Idan gwamnati ta dauki wannan matakin duk wanda bai yarda a hade wuri guda ba to yabar jahar.
Kamar yadda marigayi Sheikh Auwal Albani Zaria ke fada “babu gagararre sai bararre”.
Yana da kyau ga gwamnati tayi nazari da kyau domin tsara yadda zata tsugunnar da mazauna rugage kafin su hana zaman garuruwa da suke makwabtaka dasu kuma sune barayin sukafi yiwa illolin da suka jawo salwantar rayuka da dukiyoyin mutane. Kodai su dawo gari ko susan nayi domin kashe kashe, satar dabbobi, fyade da garkuwa da jamaa sun ishe mu.

Rubutawa:
Ado Umar Lalu, adoumarlalu57@gmail.com
Shamsu Miyetti Allah Funtua
Ahmed Bawa Faskari

Share.

About Author

Leave A Reply