Real Madrid Ta Watsa Wa Pogba Kasa A Ido, Ta Ce A Kai Kasuwa

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Rahotanni daga Kasar Sipaniya sun yi nuni da cewa, Kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid ta ce ba ta da bukatar Pogba, a maimakonsa, Mbappe na PSG ta ke so.

Rahotannin sun tabbatar da cewa, Kocin Madrid Zinedine Zidane ya gamsar da Kungiyar da hukumominta muhimmancin sayo Mbappe a maimakon Pogba.

Idan dai ba a manta ba a shekaran jiya ne Pogba ya nuna maitarsa a fili na son bugawa Real Madrid kwallo. Inda ya ce babban Burinsa kenan.

Wannan matsaya ta Madrid tamkar watsa Kasa ne ga idon Pogba. “Abin dai bai yi dadi ba.” Inji wani mai sharhin wasanni

Share.

About Author

Leave A Reply