Rikita-Rikitar Ganin Wata: Yaushe Sahun Musulmin Nijeriya Zai Daidaita?

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Muhammad Maitela, Damaturu

Rikita-rikitar ganin wata a Nijeriya abu ne wanda ya xauki dogon lokaci tare da jawo taqaddama tare da cece-kuce a tsakanin al’ummar musulmin qasa, kana mai cike da ruxani da yi wa juna kallon hadarin-kaji, rarrabuwar kawuna zuwa gida-gida, a lokacin xaukar azumin watan Ramadan da lokacin bayyanar jinjirin watan Shawwal.

Ta dalilin wannan ya jawo karkasuwar lokacin xaukar azumin watan Ramadan xin, aqalla zuwa gida biyu haka a lokacin kammala aikin ibadar, yayin da wani jiqon gardamar kan xan yi tsayi zuwa matakai har uku; kuma kusan kowa yana yi wa kan sa ra’ayin sa ne kawai daidai- tare da ganin beken xan uwan sa.

Baya ga wannan kuma, wannan al’amarin ya kai ga qarin adadin masallatan Edi- a sakamakon rarrabuwar kawunan. Lamarin da ya qara wa zaman tankiyar armashi a lokacin gudanar da ibadun da ma a bayan su.

A hannu guda, wasu sun amince su xauki azumin ko saukewa, matuqar sun amince da wanda ya ga watan, inda wasu su ka yi matsayar sai sun ga watan ido-da-ido su xauki azumin ko sauke shi don gudanar da bukukuwan sallah qarama, inda wasu su ka dogara da sanarwar Mai Alfarma Sarkin Musulmi a matsayin matakin qarshe kan ganin watan.

Duk da wannan matsayar, rikita-rikitar ba ta tsaya nan kaxai ba, sai ya kasance kowace shekara sai an tabka zazzafar muhawarar ganin watan, maimakon kowa ya tsaya matsayar shi- an wayi bari kusan kowace shekara (idan lokacin ganin watan Ramadan, Shawwal) ana samun jama’a su na sauya tunani da matsaya daga wannan ra’ayi zuwa wancan.

Har wala yau kuma, sannu a hankali kusan kowace shekara idan irin wannan lokacin ya kama sai matsalar ta xauki sabon salo- kai ka ce mahauniya. Wanda kamata ya yi ace bayan kowace qaramar sallah, malaman mu tare da shugabanin al’umma su kalli nauyin da ya hau wuyansu, su zauna wuri guda su nazarci matsalar tare da qoqarin xaukar ingantattun matakan warware ta cikin tsanaki da kwanciyar hankali.

Idan hakan ya gagara, me zai hana gwamnati ta xauki nauyin shawo kan wannan tata-vurzar, ta hanyar kafa qaqqarfan kwamitin qwararru da masana wajen lalabo mafita kan batun, saboda kowa ya huta, ya yi bacci da ido biyu!

Amma abu mai xaure kai shi ne yadda malamai da masana tare da mahukunta su ka zuba ido tare da kasa shawo kan wannan matsalar, su na kallo tana ci bal-bal tamkar wutar daji, wanda qila da sun saka baki ta kau tare da jan hankalin kowane vangare ya tsaya kan matsayar sa da ya mutunta ta xan uwan sa, ko jingine ra’ayin qashin kai wajen neman gaskiya da abinda ilimi su ka tabbatar, qila ya tsamo al’umma daga wannan kwazazzaben da su ka shiga. Amma me ya sa ba su yi hakan ba? Allah shi ne kaxai ya barwa kan sa sani!

Bisa ga tabbaci, al’amarin ganin wata ba baqon abu bane, abu ne wanda ya daxe ya na gudana a tsakanin al’ummar duniya. Sannan a kevance abu ne wanda malamai a addinin musulunci su daxe da tattauna shi a cikin littafan su- to shin an kasa gano haqiqanin yadda wannan matsalar take ko dai an bar jaki ana dukan taiki?

Qarawa da qarau, shin dukan waxannan shimfixaxxun bayanan da waxancan malaman su ka yi bai isa ya warware matsakar ba kowa ya huta? Idan kuma akwai sauran notunan da ba su tava ba, ko sun manta ba su xaure zancen nan da su ba, me zai hana a samu qwararrun masanan da za su kammala aikin, a qarqashin turbar da na farko su ke a kai? Saboda kamar na hango wasu kalaman malamai kan muhimmancin haxin kan al’umma; kar fa garin gyaran gira a tsokane ido!

Kuma idan an kwatamta matsayin ganin wata da muhimmancin haxin kan al’ummar musulmi, wanne ya fi qima da zama wajibi a mahangar musulunci?

A hannu guda kuma, idan an kalli wannan matsala, abu ne mai sauqin gaske, kuma wanda za a warware shi cikin ruwan sanyi; ba sai an tayar da jijiyar wuyan kowa ba, shin me zai hana bar masana su yanke hukunci a kan matsalar nan? Duk da wani zai yi tunanin masanan sun karkasu gida-gida, kuma qila kowane sashe da ra’ayin shi, wanda abu ne mai wuya a samu matsala, sai dai idan akwai wasu masu qoqarin rura wutar ko cin gajiyar rarrabuwar kawukan, amma kam malami uba ne!

Masu lura da al’amurran yau da kullum sun bayyana matuqar fargaba dangane da yadda matsalar ganin wata ke ci gaba da ruruwa, kuma ta na neman gindin zama kane-kane, abu yana son ya zama gado daga kakanni zuwa iyaye da jikoki tare da tattava kune, wanda a qarshe ba za ta haifar wa al’umma xa mai ido ba.

Xaya daga cikin nauyin da ya hau kan gwamnati, shugabanin addinai, sarakunan gargajiya da na al’umma shi ne su yi aikin haxa kan yan qasa. Inda Gwamnatoci za su xauki nauyin gudanar da ayyukan kalla ka koya, ingantattun manufofi da tsare-tsare da makamantan su ga yan qasa. Sanin kowa ne aikin malamai shi ne shiryar da jama’a zuwa ga samun ingantattar tarbiyyar da za ta yi amfani a kowane hali aka tsinci kai, haka na al’umma su yi qoqari wajen inganta kyakkyawar alaqa da fahimtar juna.

Wanda ko shakka babu, matuqar waxannan vangarori su na aikin da ya hau kan su, to nan gaba kaxan rikita-rikitar ganin wata da makamantan su za su zama tarihi, akasin hakan kuma sai abinda Allah ya yi. Saboda shi talaka tamkar ta-maula (qwallo) yake, ba shi da qafafu ballantana ya kama qasa; duk inda ka zungure shi da qafa gungura wa zai yi!

A qarshe, ya na da gayar muhimmanci gwamnatocin mu, sarakunan gargajiyar mu, shugabanin addinai da na al’umma su farka tare da xaukar matakan yayyafa wa wannan matsala ruwan sanyi- saboda idan har yanzu mun kasa magance rikita-rikitar ganin watan Ramadan da Shawwal, to sai yaushe za mu tunkari manyan matsalolin ci gaba a qasar mu da al’ummar mu? Alhali muna al’umma mai bin addini guda xaya?

Saboda tarihi babu ruwan shi, kullum naxa yake yana taskace abinda hannayen mu ke aikata wa!

 

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply