RTEAN Za Ta Tabbatar Da Nasarar Samar Da Motoci Masu Amfani Da Iskar Gas A Nijeriya—Musa Maitakobi

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Daga Bello Hamza

A makon jiya ne Shugaban kungiyar Sufuri ta RTEAN Ambasada Dakta Musa Maitakobi ya samu nasarar lashe zaben zama Ma’ajin Kungiyar Kwadago ta TUC, wannan ba karamin nasara bace, wakilinmu Bello Hamza, ya tattauana na shi inda ya tabo al’amurra da dama da suka shafi harkokin kungiyar da yadda ya shirya bunkasata ta yadda za ta yi daidai da zamanin da muke ci, ya kuma yi bayanin halin da ake ciki a kan shirin samar da motoci masu amfani da iskar gas. Ga dai yadda hirar ta kasance.

Ya kuma sharya tabbatar da samuwar iskar gas din don amfanin motocin da aka kaddamar?

Zamu nemi filaye a wuraren da muka ga ya dace don gina wannan gidajen mai, Insha Allahu zamu gina. Bankin Kasa ya kira mu mun zauna dashi ya kuma ce mu kawo tsarin mu yadda Yakamata mu yi su gani, na biyu akwai kanfanoni masu zaman kansu da hadin guiwar representatibe na ministan cikin gida a bangaren man fetur suma ina tabbatar maka sun zo mun zauna da su mun yi bayanai na gamsuwa na inda ya dace da inda za’a gina wannan da kuma share da za a bayar. Daga kan su membobi da kanfanoni da za su shigo wannan tafiya.

Babban bankin shi zai baku kudin da za a gina wadannan wuraren gidajen mai na wadannan motoci, koko akwai wani karin kudi?

A Yanzu na gaya na akwai kafanoni guda biyu, da wani dream energy, Wanda suna cikin wannan tafiya. Amma har zuwa yau maganar cewa bankin kasa ko Akwai wani kudi da ya ware don ya bamu don ayi wannan aiki, tukunna. Muna dai zama dasu suma hanyar da suke ganin zasu taimaka toh zasu taimakawa. Lokacin ma’ana abun da nake nufi Aban duk lokacin da suka fito suka gaya mana ga irin taimakon da zasu bamu, na kudi ne, na bashi ne da ruwa, ko ba ruwa, duk bazan iya baka labari ba domin bamu gama zama dasu ba.

Kenan ida na fahimce ka kungiyar RTEAN na kasa ce za ta dauki nauyin wannan aiki?

Eh ba kungiya ce kadai zata dauki nauyin aikin ba, tare da wadannan kanfanoni da na zana maka zamu hadu mu dau nauyin wannan aiki da zamu yi.

Ina aka kwana game da maganar bhayar da keke masu tayoyi uku don tallafa wa al’umma?

Muna nan akai saboda dalilin haka ma muna tabbatar maka zamu yi tafiya zuwa wani kamfani a Koriya Saboda shi wannan keke da kake gani Bajaj, muna son a sake masa tsari ne. A maimakon yana bude, mukan so ya koma yana rufe, a rufen Kuma maimakon Mutum uku kawai yake dauka a baya wanda muke don ya zama yana daukan mutum bakwai ko shida. Tsari muke so za a yi masa ya zama kafa hudu kamar mota. Dalili duk inda wancan mai kafa uku zai shiga shima zai shiga lungun. Baya haka yanayin yadda muke ganin mata suke shiga wannan keke abun bai burge mu, bai bamu sha’awa. Dukkanmu mun san yanayin yadda mace ke zaune in ta zauna. Wannan keke bai da kofa, bai da kariya Kuma tampolin din da yake genfen ta Nan da nan ba sakin sa ake ba.

Toh mun ga wannan Yakamata ace idan an samu wannan short robust din wacce take daukan mutum shida zasu iya amfani da ita a maimakon ma wannan keken. Kuma zai zama Akwai tsari Akwai kuma suturcewa. Toh wannan shine abun da muke kai. Kuma muna sa ran ba da dadewa ba, Allah zai bamu ikon yadda zamu kaddamar da abun kuma mu tafiyar dashi cikin ikon Allah.

Bari mu koma kan batun Faret na kasa wanda kungiyar RTEAN ta kasa ta gudanar a filin wasa na MKO Abiola watan da ya gabata wanda wannan fareri masana harkokin sanin kungiyoyin sufuri sun tabbatar da cewa ba’a taba yin irin shi ba tun da aka kafa wannan kungiya?.

Toh ai dani dakai mun san halin da kasar nan take ciki, kuma bai dace a ce mun bar ma gwamnati hakkin abun da ya shafi tsaro kadai ba, mu kanmu muna da rawar da zamu taka a ciki, wannan shi ya jawo hankalin mu muka ga cewa ya dace a wannan gaba mu tabbatar cewa mun training membobinmu Wanda muke kira RTEAN Martial Wanda za su yi aiki. Kafada kafada da jami’an tsaro. Na farin kaya ne, wanda suke sa uniform ne? Ko ma ya ta kaya, numa muna son a matsayin mu na yan Nijeriya, a matsayin na masu kishin kasar mu mu tabbatar da cewa mun bayar da namu kason a wannan fage da ake ciki, kuma kada ka manta a baya mutane na zargin cewa wasu bata gari sukan bi ta hanyar tashar mota inda suke zuwa da wasu abubuwa da suka shafi kwayoyi, abun da ya shafi alburusai, bindigogi ko mene dai ana zargin cewa ana biyo dasu ta tashan motoci. Toh da wannan dogarwan da muka sa ba zai yiwu ba domin duk abun da kazo sai an tantance. Toh wannan shi abun da ya jawo hankalin mu kenan muka ga cewa ya dace mu kada wannan kungiya tamu dama akwai ta bawai babu ba. A duk inda kaje gareji zaka shiga mota zaka ga akwai su amma mun sake daga ta ta batun cewa jama’a su sani cewa fa wannan kungiya tana nan, amma yanzu mun sake habaka ta, ta yadda duk jami’an tsaron da suka wannan kasa zasu san Akwai wannan kungiya akwai kuma wannan Martial na wannan kungiya wanda zasu iya hada kai dasu akan cimma wasu burika abun da ya shafi tsaron rayukan Mutane da duniyoyin su.

Wace irin nasara kake ganin an samu cikin wannan takaitaccen lokaci?

Ina tabbatar maka an samu nasara mai dimbin yawa, Nasarar kuwa itace, yanzu muna tuntubar juna. Kuma mun rubuta takardu zuwa jihohi saboda muna kiran cewa tsakanin su martial namu da jami’an tsaro da gwamnatin zartarwa ta state din, azo a hada karfi da karfe. Kafada da kafada domin duk inda ake Ganin za’a toshe a toshe, duk inda ake ganin ya tsage ayi kokarin a face shi toh muna nan akan wannan damu dasu. Toh abu ne wanda ka sani dole ne duk abun da aka ce tasro ne dukiyoyin mutane da rayukan su abu ne Wanda Yamamata a bashi da hankali. Ko bature na yana cewa ‘slow and steady’ . Toh Amma idan aka bi a hankali kamar yadda muke bi muna tuntubar junan mu su kansu yayan kungiyar wanda ake ce masu RTEAN martial dole ne zasu samu horo ta wani bangare a bangaren jami’an tsaro dole ne zasu samu wasu shawarwari wajen shugabannin tsaro na kasa wanda wannan zai basu kwarin guiwa a bangaren kware wa su tafiyar da Ayyukan nasu a duka i da gareji yake ana lodi, lodin kaya ne ko fasinja. Zasu samu horo domin sanin Yadda zasu gudanar da ayyukan su da kuma gane mai laifi da kayan da aka sa abun laifi da wanda ba’a sa abun kaifi ba. Idan baka manta ba na fada na dole ne zamu nemo scanner Wanda itace zata gane mutum ko yana dauke da wani abu a jikin sa ko babu. Ko kuma a kayan mutum akawai wani abun cutarwa wanda ka sa ka boye a gane cewa akwai wani abu a ciki. Duk wannan hanyoyi sune muke shirye shirye akai kuma muna tabbatar na Al’umma cewa dari bisa dari muna tare dasu kuma mun tabbatar da cewa duk irin yadda suka bamu shawarwari na yadda zamu tafiyar da wannan RTEAN martial dinnan zamu karba hannu biyu.

Kun gamsu da yadda dogarawan naku suka fara gudanar da aiki zuwa yanzu, ko akwai wasu kurakurai da kuka gano?

Wadannan motoci yawancin su a shiyyar kudu ne maso yamma suka fara aiki, basu fara a arewacin Nijeriya ba. Wannan ya nuna kenan cewa su shuwagabannin kungiyar na Arewacin Nijeriya basu da wannan karfin da zasu iya siyan  wadannan motoci koko ya abun yake?

A’a al’amarin ba haka yake ba ai wanda ya fara biya shi ake fara ba. Suma suna yin iya kokarin su wanda yake da yawa daga cikin su wasu suna nan da shirin zasu turo da kudaden su na iya yawan motocin da suke so amma dai wadannan wanda na gaya maka daga kaddamar wan mu sati guda suka biya kudaden wasu motoci wanda suke so, kuma a bisa tsarin doka mun basu motocin su kamar yadda suka biya suma Kuma namu na arewa suna nan suna ta shirye shirye wanda yake kasan yanayin karfin Arewa a ɓangaren abun da ya shafi tattalin arziki na kasa na shige da fice na Arewa da kudu ba daya bane so amma namu su kansu suna kokari kuma Insha Allahu ina tabbatar maka nan ba da jimawa ba Zaka ji motocin nan a kowani state sun karbi nasu.

Ran ka ya dade wani tallafi kuke samu ko kuma kwarin guiwa da goyon baya daga bangaren gwamnatin tarayya?

Toh Gwamnatin tarayya in dai ta dauki kudi ta bamu ai zamu fada maku, in kuma ta ba mu wani tallafi zamu gaya muku, koda waiber ne aka bamu zamu gaya muku cewa ai an yarda mu shigo da motoci kaza amma aka abin da zamu biya duty a rage mana kaza, zamu sanar daku. Amma har zuwa yanzu babu ko taro ko anini ko kwandala da ya fito daga ɓangaren gwamnati cewa ga wannan an bamu a taimaka mana dan saboda wannan motoci na Png da za su yi aiki ma’ana mu bada kason da aka nema a wajen mu, mu dai bamu samu wannan tallafin ba.

Amma tun da kuka kaddamar da wannan motoci kun gayyato ministan sufuri a Wannan wuri domin ta shaida wannan al’amari, wannan yana nuna cewa kenan ma’aikatan sufuri bata tallafa maku ba kan wannan al’amari?

To ai ina ta tallafa ma a zan gaya maka, sai dai in kana nufin tallafi na cewa mun gayyace ta ta zo. Yawwa in wannan tallafin kake nufi to yazo ta tallafa mana, amma in dai tallafi ne na kudi ko kuma bashi ba tare da ruwa mai yawa ba. Toh gaskiya babu.

Toh ranka ya dade ina maganan Conbertion Center da kuke maganan Gwamnati ta samar da wurare inda za a yi conbersion center.

Conbersion center ai bashi da wahala,abin da muka ce shi ne, cewa zamu samar da gidajen mai wanda za a iya samun CNG da LNG da na diesel din a ciki petrol station din duk a cikin gidajen mai kuma a matsayin da yanzu muke kokarin sanar da kai muke kai, cewa mun zabi jihohin Zone shida na kasar nan uku a kudu, uku a Arewa.

 

 

 

 

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply