Rundunar ‘Yan Sanda Ta Legas Ta Aika Da Jami’ai 1,000 Edo Don Zaben Gwamna

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Rundunar ‘yan sanda ta Legas ta aika da jami’anta 1,000 da za su taimakawa sauran jami’an tsaro wajen tabbatar da oda yayin zaben gwamnan da za a yi a Edo ranar 19 ga Satumba.

Hakan ya fito ne cikin sanarwar da Kakakin rundunar, SP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar a Legas ranar Lahadi.

Adejobi ya ce Kwamishinan ‘yan sanda na Legas, Hakeem Odumosu ya shawarci jami’an da sun una kwarewa yayin gudanar da aiki a wajen zaben.

“Ya kuma jadadda aniyar Sufeto Janar din ‘yan sanda wajen kare muradun dimokuradiyya na zaben gaskiya,” inji kakakin.

Odumosu ya ce  Sufeto Janar din ya bada damar kayan kulawa da jin dadin  jami’an don gudanar da aikin na musamman.

Kwamishinan ya bukaci jami’an da su kare kansu sannan su guji aikin da zai jawo wa Rundunar bakin jini ko kuma zai kawo tsaiko wa zaben jihar Edo, inji sanar sanarwar.

 

Share.

About Author

Leave A Reply