Sabi’u Tunde : Shugaba Buhari Da Hayaniyar Masu Mugun Nufi, Daga Gidado Ibrahim

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Rubuce yake a tarihi cewa, duk yadda gwamnati ta kai wurin yin kokari domin magance matsalolin da gwamnatocin baya suka gadar mata, sai an samu wasu da za su rika yi wa wannan yunkuri kafar ungulu. Su kan yi hakan ta hanyar yada karairayi marasa tushe.

Ta bayyana karara cewa babbar manufar wasu kafafen sadarwa na intanet shi ne su haifar da tarnaki da matsala ga gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. A wani rahoton kwanannan da wata kafar sadarwa mai suna ‘People’s Gazette’ ta fitar, tana zargin wai Shugaba Buhari ya nada dan wansa, Sabi’u Tunde Yusuf a matsayin mataimakin Daraktan NIA.

Na kasance daya daga cikin masu harkar hulda tsakanin kasa da kasa na tsawon lokaci, wanda hakan ya bani damar ziyartar kasashe mabambanta, kuma na ziyarci gidajen gwamnatoci a yammacin turai. Mafi yawa na masu tallafawa Shugabannin wadancan Kasashe za ka taras jami’an tsaron sirri ne ko na fararen kaya. Don haka ai ba ma wani laifi ba ne a tashin farko don Sabi’u Tunde ya zama memba na daya daga hukumomin tattara bayanan sirri.

Tana iya yiwuwa wanda ya wallafa wannan shirmen bai san ka’idar aikin gwamnati ba, ko kuma ya aikata hakan ne da gangan. A tashin farko ma ai kundin tsarin mulkin Nijeriya bai yi hani ga shugaban kasa ya ba ‘yan uwansa aiki ba, matukar sun cancanta. Shin su ba ‘yan Nijeriya ba ne? Tana iya yiwuwa jaridar People’s Gazette a kokarinta na watsa sharri ta manta cewa shugaban Kasar Amurka da ya sauka, Donald Trump ya nada sirikinsa, Mista Kushner, wanda bai taba aikin gwamnati ba a matsayin babban mai ba shi shawara.

Mista Kushner ya taka muhimmiyar rawa a gwamnatin Trump, ta yadda har ta kasance ma shi ne mai shiga tsakani a yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla kwanan baya tsakanin Isra’ila da Kasashen Larabawa. Kushner ba shi da wata kwarewar aiki da ta wuce kula da kasuwancin saye da sayar da gidaje na mahaifinsa. Shin an samu irin wadannan kananan maganganun da gutsiri tsoma a Amurka don kawai Trump ya nada sirikinsa a wannan matsayi? Tunda Surikin nasa na da kwarewar da zai iya yin aikin da aka ba shi, babu wata damuwa a hakan.

Idan muka kalli Amurka a tsanake, wacce daga wurinta Nijeriya ta aro tsarin gudanar da mulki. A shekarar 1993, Shugaba Bill Clinton ya nada matarsa Hillary Clinton a matsayin Shugabar da za ta jagoranci tsarin yin garanbawul ga sashen lafiya.

Haka nan kuma, John Adams, wanda shi ne shugaba na biyu a jerin shugabannin Kasar Amurka, ya bayar da babban mukami ga daya daga cikin ‘yan uwansa. Adams ya nada dansa, John uincy a matsayin Ministan Amurka a Prussia a shekarar 1797, wanda dai dai yake da Ambasada a yanzu. Idan da a Nijeriya ne haka ya faru, da yanzu Jaridar People’s Gazette tana nan ta watsa sharri da kazafi marar asali. Haka nan kuma Shugaba Adamsa ya nada surikinsa, William Stephens Smith a matsayin mai kula da tashar ruwa ta New York a shekarar 1800.

Akalla shugabannin Amurka shida ne suka nada ‘yan uwansu na jini a mukamai manya, irinsu James Madison, James Monroe, Andrew Jackson, John Tyler, James Buchanan, da kuma Ulysses Grant.

Franklin Roosevelt ya nada dansa James a matsayin mai taimaka masa a watan Janairun shekarar 1937. Bayan watanni shida, a ka yi wa James karin girma zuwa Sakataren Shugaban Kasa. A Oktoba ta wannan shekarar aka karawa James mukami inda ya zama Ko’odinetan Fadar ‘White House’ mai kula da ma’aikatu 18.

A watan Oktobar 1958, Shugaba Dwight Eisenhower ya nada dansa, John a matsayin mataimakin Sakataren fadar ‘White House’. A wancan lokacin John soja ne da ke da mukamin Manjo.

Shugaban Amurka John Kennedy ya nada dan uwansa, Robert a matsayin Alkalin Alkalan Amurka a watan Janairun 1961. Haka nan kuma Kennedy ya nada surikinsa, R. Sargent Shriver a matsayin Daraktan ‘Peace Corps’ a watan Maris din 1961. Daga wadannan jerin misalan, Don Allah a ina ne Buhari ya yi kuskure? Ko kuma a ina ne ya aikata ba daidai ba?

Su a haukarsu, Jaridar People’s Gazette ta ce, saboda a boye abin ne ma ya sa Shugaba Buhari bai sanar ba. Shin so suke yi sai Shugaba Buhari ya je gidan rediyo ya sanar da duk wani nadi da ya yi a gwamnatinsa?

Saboda tsabar karya da rashin abin fada, jaridar ta ci gaba da zargin wai Tunde tare da hadin bakin tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnati, Marigayi Abba Kyari sun kwace lamarin kula da takaddamar manoma da makiyaya wanda da ke hannun mataimakin shugaban kasa. Wai sun yi amfani da hakan wurin fitar da kwangilar Naira Biliyan 12 da sunan gina RUGA. Kaitsaye, ana iya cewa, irin wadannan karairayi na People’s Gazette za su iya zama barazana ga harkar tsaron Nijeriya.

Zarginsu na cewa wai Shugaba Buhari na nuna wariya zancen banza ne, domin kuwa da zuwansa ofis a shekarar 2015, ya nada Kemi Adeosun a matsayin minister kudi. Ya nada Gabriel Olanisakin a matsayin shugaban rundunar soja. Bayan ritayar shugabannin rundunonin tsaro a ‘yan kwanakin nan, muna ganin yadda aka nada har da dan kudu a cikin sabbin shugabannin.

FIRS na daya daga cikin muhimman ma’aikatun da a ke da su, a 2015, shugaba Buhari ya nada Babatunde Fowler a matsayin shugaba.

Shugaba Buhari ne ya yi tsayin daka wurin ganin an yi duk mai yiwuwa don Ngozi Okonjo Iweala ta zama Shugabar Cibiyar Kasuwanci ta Duniya. Shin Ngozi ‘yar arewa ce?

Ina jaddada cewa, babu wani laifi ko saba ka’idar aiki a ba Tunde aikin mai taimakawa Shugaba Buhari. Sannan duk sauran kazafi da kagen da jaridar ta yi, ba komi ba ne face neman kafar watsa sharri da tayar da hankalin al’umma.

– Ibrahim shi ne Daraktan Sadarwa da Tsare-tsare na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa (PSC).

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply