Sarkin Gombe Ta Bukaci Karin Zaman Lafiya Tsarkanin Manoma Da Makiyaya

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu III, ya bukaci makiyaya da manoma su nisanci tashin hankali a tsakaninsu su kuma rungumi akifar zaman lafiya.

Sarkin ya yi wanna bayani ne yayin da Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Inuwa Yahaya ya kai masa ziyara ban girma a fadarsa a cigaba da bukuwan sallah.

”Ya kamata makiyaya da manoma su zauna lafiya da juna saboda suna da matukar mahimmanci ga bunkasar tattalin arzikin kasar nan gaba daya,” inji shi.

Ya kuma bukaci al’umma su cigaba da yi wa kasar nan addu’ar zaman lafiya tare da maganin matsalar tsaron da ake fuskanta a halin yanzu a sassan kasar nan.

Ya kuma jaddada bukatar al’umma Musulmi su yi amfani da darussan da suka koya a lokacin azumin watan Ramadan, da kuma amfani da wa’azozin da malamai suka gabatar a cikin watan wajen bunkasa raywar su da kuma samar da hadin kai don cin gajiyar ribar dimokradiyya a dukan matakai.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya bamu damina mai albarka.

 

Share.

About Author

Leave A Reply