Shekara 60 Da Samun ‘Yanci: Jawabin Buhari Ya Farfado Wa ‘Yan Nijeriya Da Fata

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Sakataren watsa labarai na jam’iyyar APC a Akwa Ibom, Mista Nkereuwem Enyongekere, ya ce jawabin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ranar Alhamis ya farfado wa ‘yan Nijeriya da fatan cewa kasar za ta kai ga ci.

Enyongekere ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da manema labarai a Uyo ranar Alhamis da yake sharhi kan jawabin bikin cikar kasar shekara 60 na kasar.

 

Ya ce jawabin da shugaban kasar ya yi kira ne ga ‘yan Nijeriya da su zo a hada kai, a rungumi abin da ya hadamu.

“Jawabin shugaban kasa ya tafi da kuma, saboda ya waiwayi baya, yau da kuma gobe, inda ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su zo a gina sabuwar kasa.

“Duk da kutsen da sojoji suka yi na shekara 29, amma akwai abubuwan farin ciki a kasar.

“Jawabin ya nuna dattako da gaskiyar Shugaban da ke kira kowanne dan kasa ya zo a tafi tare da shi.

“Jawabin na shugaban kasa ya dada tabbatar dacewa na Nijeriya ta shiga shekarun zinare ne,” inji shi.

Ya bukaci ‘yan Nijeriya da su rungumi kiran da shugaban kasa ya sauya tunani, don a fara tunanin kasa a kowanne yanayi kafin yankunanmu.

Sakataren watsa labaran ya yi kira ga dukkan ‘yan Nijeriya daga kowacce jam’iyya da su zo a mara wa gwamnatin da Buhari yake jagoranta baya, da fatan cewa kasar za ta kai ga matakin nasara.

 

Share.

About Author

Leave A Reply