Shiriritar ’Yan Adawa Dangane Da  Yada Karyar Rikicin Cikin Gida A Villa, Daga Gidado Ibrahim

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Babban aikin jam’iyyun adawa shi ne gabatar da suuka kan abubuwan da za su taimaka wa masu gudanar da mulki da nufin zaburantar da su, yadda za su kara kumaji wajen tafiyar da harkokin mulkin al’umma. Babbar manufar adawa shi ne hada hannu da masu tafiyar da mulki don samun kasa ta gari. Amma abin takaici shi ne yadda ‘yan adawa a Nijeriya suka mayar da harkar adawa ta zama abin dariya wacce ba a taba ganin irinta a harkar mulkin dimokradiyya ba a duk duniya, musammna ganin suna sanya son rai ne a kan sukar da suke yi wa gwamnati.

Daya daga cikin abin takaici na baya-bayan nan da ‘yan adawar Nijeriya suke yawo da shi ne batun matsalar tsaro da aka samu a fadar shugaban kasa, inda aka bayar da rahoton wai an yi harbe-harbe a fadar shugaban kasa ta ‘Aso Rock’ bayan da aka samu rashin jituwa tsakanin Iyalin Shugaban Kasa da wasu jami’an fadar shugaban kasar.

Babban abin takaicin shi ne yadda ‘yan adawar Nijeriya suka kasa gane mene ne ake kira da matsalar tsaro. To da farko ma bari mu tamabaye su, mene ne matsalar tsaro? Wannan matsalar farko da ‘yan adawan ya kamata su fayyace wa al’umma kenan, ba wai su shiga kafafen watsa labarai su yi ta babatu kan abin da ba su da masaniya a kai, bayanan da suka yi a kafafen watsa labarai ya kara fito da jahilcinsu akan al’umuran da suka shafi tsaro da tafiyar da mulki.

A wasu wuraren da ‘yan adawa suka san abin da suke yi, suna daukar al’amurran tsaro da matukar muhimmanci, ba su shigar da abin da ya shafi tsaro cikin siyasa, saboda a bayyane lamarin yake cewa, adawa daban kuma tafiyar da kasa ma daban. Duk wanda yake kokarin hada matsalar tsaro da harkar adawa yana neman kawo babbar baraka ne a kasar, kuma kansa matsalar za ta koma.

A inda harkar adawa ta amsa sunanta, za ka samu ‘yan adawa na mayar da hankali wajen fadakar da gwamnati wuraren da aka samu matsala akan abubuwan da suka shafi tafiyar da gwamnati da kuma yadda za a aiwatar da manufofin da gwamnati ta yi alkawarin aiwatarwa na bunkasa rayuwar talaka, ta haka za a samu ciyar da kasa gaba haka kuma zai tabbatar da bunkasar tattalin arzikin al’umma gaba daya.

Wasu daga cikinmu da muka san yadda harkokin tsaro ke tafiya muna sane da cewa, lallai akwai wasu dake yada zantukan teburin mai shayi, daga cikin fadar shugaban kasa wadanda suna take-taken ganin wannnan gwamnati ta shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gaza cimma manufofinta, cikin hanyar da suka shirya cimma wannan burin shi ne ruruta duk wata matsala da suka sunsuno a cikin fadar shugaban kasar. Ta yadda ‘yan adawa za su yi amfani da matsalar wajen yamadidinsu.

A tarihin Nijeriya babu wata gwamanati da ta taba samar da kwararrun jami’an tsaro a matsayin ma’aikata a fadar shugaban kasa kamar mulkin shugaba Muhammadu Buhari. Ba zai yiwu a samu matsalar tsaro a fadar shugaban kasa ba alhali irin su mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Muhammed Babagana Mongonu (rtd) suna nan, wanda an tabbatar da kwarewarsa a fannin tsaro bisa la’akari da yadda ya gudanar da ayyukansa a baya, saboda haka samar da tsaro a fadar shugaban kasa a wajensa wani aiki ne mai saukin gaske.

Haka kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari mutum ne tsayayye da ya san aikinsa, kuma su biyu ne suke tsara lamarin samar da tsaro a fadar shugaban kasa.

Wai shin ma dole ne sai mutum ya yi suka da sunan adawa ko da ba shi da wani abu da zai yi magana a kai? Lallai ya kamata mutum ya yi shiru da bakinsa idan har ba shi da abin da zai fada mai muhimanci. Ya kamata su je su dauki darasi a Cibiyar Tsaro ‘Institute of Security’ da ke Geneva. Don su san me a ke kira da matsalar tsaro kafin su nuna wa al’umma tsananin jahilcinsu.

Babban abin takaicin kuma shi ne yadda aka sanya karya a cikin batun gaba daya, a sanarwar manema lanarai da ‘yan adawar suka bayar, wai sun nuna damuwar su akan matsalar rashin jituwa a tsakanin uwar gidan shugaan kasa, Aisha Buhari, da da kuma wasu jami’an fadar Shugaba  Buhari. Wai har abin ya kai ga bata-kashi tare da harbi da bindiga a fadar shugaban kasa. wannan karya ne kuma abin takaici, an kuma sharata ne don a rudar da al’umma, wai kuma ana haka ne don a jawo ra’ayin mutane.

Abin lura a nan shi ne, al’ummar Nijeriya sun gano badakalar ‘yan adawar Nijeriya, sun kuma san matsayinsu na rashin kishin kasa, suna kuma sane da cewa, babban burin ‘yan adawar shi ne ganin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu matsala, musamman shirin nan da shugaba Buhari ya yi na ‘Next Level agenda for Nigeria’.

Jam’iyyar da ta yi shekara 16 tana tatsar arzikin Nijeriya ba tare da wani ayyuka na azo a gani ba har ta sami bakin bayyana cewa, “Wannan lamarin da ya faru a gwamnatin Buhari ya fito da rashin ingancin lamurran tsaro a fadar shugaba kasa kuma yana nuna matsala akan masu tafiyar da harkar tsaron, wai wannan wani sakacin aiki ne, da ya kai ga matsalar tsaron da aka samu”, lallai wannan koluwar matakin munafunci ne, dama  ‘yan Nijeriya sun gaji da soki burutsun a yada suke fuskantar al’amurra.

Wai shin ba su ne suka jefa kasar nan cikin matsalar tattalin arzikin da ake fuskanta ba? hatta matsalar tsaron da Shugaba Buhari ya gada ai sakacin mulkin su ne na shekara 16 ta jefa kasar nan cikin rashin tsaron da ake fuskanta.

Zan sake jaddadawa don ya shiga can cikin kwakwalwar ‘yan adawa, cewa, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari da mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Janar Muhammed Babagana Monguno suna nan daram suna tafiyar da al’amurran tsaro a fadar shugaban kasa dama fadin tarayyar Nijeriya gaba daya yadda ya kamata. Koma bayan korafin da suke yi na cewa, akwai gaggarumar matsalar tsaro a fadar shugaban kasa ta ‘Aso Rock’ ko kuma wani waje a fadin tarayyar Nijeriya.

Ya kuma kamata al’umma su gane cewa, ‘yan adawan suna haushi ne na kulle su da aka yi har abada da fagen mulkin kasar nan, an yi hakan ne kuma saboda yadda suka mayar da cin hanci da rashawa ruwan dare a kasar nan a zamanin mulkinsu.

Fiye da kowanne lokaci a fadin kasar nan an samu cikakken tsaro, an samar da tsaro a fadin kasar nan fiye da kowanne lokaci. Tawagar shugaba Muhammdu Buhari za su samu nasara duk kuwa da kokarin kawar da hankulansu da ake neman yi ta hanyar miyagun ayyukan ‘yan adawa. Shawara ta ga ‘yan adawa shi ne su fahinci cewa tasirinsu ya riga ya dushe, al’ummar Nijeriya sun gane cewa, basu da sauran nauyi a fagen tafiyar da mulkin Nijeriya.

Ya kuma kamata su gaggauta tuba tare da bada hakuri ga ‘yan Nijeriya akan gazawarsu su kuma gagauata kowa su dauki darasin yadda ake adawa mai tsafta bana soki burutsu ba.

  • Ibrahim shi ne Daraktan sadarwa da tsare-tsare na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa ‘Presidential Support Committee’

 

Awesome
  • User Ratings (0 Votes) 0
Share.

About Author

Leave A Reply