Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Wayar Salula Ta Farko Da Aka Kera A Nijeriya

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A ranar Laraba ne Shuganan kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci kaddamar da wayar salula ta farko da aka kera a Nijeriya mai suna  ITF Mobile.

Ministan masa’anantu da zuba jari, Adeniyi Adebayo, ya gabatarwa da shugaban kasar wayar kafin gudanar da taron majalisar zartaswa ta kasa a Abuja.

Ya kuma sanar wa shugaban kasar cewa, wayar na daga cikin jerin wayoyi 12 da ake shirin kerawa inda aka yi amfani da kayyakin da ake samu a cikin gida wajen aikin kerawa, wanda hukumar ‘Industrial Training Fund’s (ITF) Model Skills Training Centre’ ta jagoranci aikin kerawa.

Wadanda suka kasance a taro sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da kuma shugaban ma’aikata a fadar shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari.

Sauran sun kuma hada da ministan yada labarai, Lai Mohammed; minstan kudi, Zainab Ahmed, da ministan shari’a, Abubakar Malami.

Share.

About Author

Leave A Reply