Shugaba Buhari Ya Nemi Gwamnoni Su Rungumi Ayyukan Cigaban Al’umma

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A jiya Alhamis ne Shugaba Muhammadu Buhari, ya xora wa Gwamnonin Nijeriya alhakin ci gaban jihohinsu da ma qasa baki xaya.

Shugaban ya bayar da wannan umarnin ne a lokacin da ya ziyarci mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado-Bayero, jim kaxan bayan kammala bikin shimfixa layin dogo daga Kano zuwa Kaduna.

A cewarsa, “ina nan kano don ganin wasu ayyukan da wannan gwamnati mai ci a qarqashin Gwamna Abdullahi Ganduje ta yi, kuma na yi farin ciki da abin da na gani,  domin Gwamnan na qoqarin ganin cewa ba a bar jihar a baya ba.”

Shugaban qasar ya qara da cews, “Kano na iya yin takara da wasu a duniya, saboda himmar da Gwamnan ke yi, wanda ya sadaukar da kansa don kammala ayyukan da gwamnatocin baya suka bari.”

Shugaban ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa wajen tsara manufofi da shirye-shirye da nufin xaukaka darajar rayuwar ‘yan Nijeriya.

Tun da farko, Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce, sadaukarwa da jajircewar da gwamnatin tarayya ta yi wajen farfaxo da harkar sufuri, wata manuniya ce ta yadda tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba.

Ya bayyana cewa, tasirin cutar Korona ya shafi tattalin arzikin duniya baki xaya.

Ya ci gaba da cewa, gwamnatinsa za ta yi duk abin da take iyawa don samar da isasshen tsaro, ilimi kyauta da tilas da kiwon lafiya mai inganci da sauransu.

Ganduje ya ce, “na yi farin ciki game da aikin layin dogo daga Kano zuwa Kaduna wanda zai bunaasa ayyukan tattalin arziki da kuma farfaxo da vangaren sufuri.”

Shima da yake jawabi, Mai martaba Sarki Ado-Bayera, ya umarci shugaban qasar da ya qara qaimi wajen magance matsalar rashin tsaro da tattalin arziki.

Ya bayyana Buhari a matsayin shugaba na qwarai, don haka ya buqaci ‘yan Nijeriya su dage da addu’o’i domin tsaro da haxin kan qasar.

“Muna godiya ga shugaban qasa kan ayyukan ci gaba a duk faxin qasar nan, musamman jihar Kano. Ina fatan ‘yan Nijeriya za su tallafawa qoqarin gwamnatoci ta hanyar zama masu sa ido a cikin al’umma,” in ji Sarkin.

Share.

About Author

Leave A Reply