Shugaban Majalisar Dattawa Ya Nuna Damuwarsa Kan Hare-haren Da Ake Kaiwa Gidajen Yarin Kasar Nan

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya yi tir da yadda aka kai hari babban gidan yarin garin Imo da kuma wasu ofishoshin ‘yan sanda a jihar.

Bayanin haka na kunshe ne a takardar sanarwa da Mr Ola Awoniyi, jami’in watsa labaran shugaban majalisar dattawan ya sanyawa hannu aka kuma raba wa manema labarai, ya kuma ce, harin wani aiki ne wadanda basu san ciwon kansu ba, kuma makiyar kasar nan ne gaba daya.

Shugaban majalisar ya bayyana haka ne a garin Owerri ranar Juma’a a yayin da ya ke kaddamar da wasu ayyukan raya kasa da Gwamna Hope Uzodinma ya yi wa al’umma a jihar Imo.

Ya kuma ce, babbar burin wadanda suks  kai harin shi ne na neman kawar da hankalin gwamnatin jihar da kuma gwamnatin tayarra akan akin da ta sa a gaba na binkasa rayuwar al’umma.

Wata hanyar da aka sanya wa sunan tsohon shugaban majalisar dattawa marigayi Chief Evan Enwerem, na daya daga cikin ayyukan da aka kaddamar don bikin cikar Gwamna Uzodinma shekara 1 a ofis.

Sanata Lawan ya shawarci al’umma da su kula da ayyukan da gwamanati don don su ne aka yi ayyukan su ne kuma ya kamata su kula da ayyuukan.

“Tabbas ya kamata jami’an tsaronmu su kara kaimi wajen kare rayuwar al’umma, za kuma mu cigaba da tallafa wa rundunonin tsaronmu don su samu nasarar da ake bukata,” inji shi.

 

Share.

About Author

Leave A Reply