Shugaban Qaramar Hukumar AMAC Ya Raba Tallafin Karatu Na Naira Miliyan 28.7

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A jiya Alhamis ne qaramar hukumar Abuja Municipal Area Council (AMAC) ta ba da tallafin karatu na kimanin Naira miliyan 28.7 ga xalibai dubu xaya daga qaramar hukumar, gami da waxanda ke karatu a manyan makarantu daban-daban a faxin qasar.

Shugaban qaramar hukumar AMAC, Abdullahi Candido, a lokacin da yake gabatar da tallafin ga waxanda suka ci gajiyar tallafin a sakatariyar qaramar hukumar da ke Abuja, ya ce, an ba su kyautar ne domin karatunsu na shekarar 2021.

Candido ya ba da tallafin karatu ga wasu yara a wasu makarantun firamare a cikin qaramar hukumar, waxanda suka shiga gasar kacici-kacici a farkon wannan shekarar.

A cewar shugaban, kyaututtukan tallafin karatun na daga cikin qudurin gwamnatinsa na tallafa wa ilimi da qarfafa wa xaliban gwiwa.

“Abin da ya fi muhimmanci a gare mu shi ne mu ba da cikakkiyar kulawa ga ilimin ‘ya’yanmu. Qanqanin da abin da muke ba ku na nuna hazaqar da iyayenku ke yi ne. Ko da iyayenku ba su da kuxin da za su tura ku makaranta, da fatan za ku koyi wasu dabaru don ku sami kuxi don tura kanku makaranta,” in ji shi.

Tun da farko, Shugaban sashin Ilimi a AMAC, Dakta Sheriff Amjnu, ya ce, an zavi xaliban da suka cancanta daga unguwanni 12 na qaramar hukumar kuma an ba da fom xin neman kyauta.

Ya qara da cewa, daga cikin aikace-aikace 1,400 da aka karva, an ga ‘yan masu nema 1,000 waxanda suka cancanta kuma an zave su don kyautar karatun.

A cikin jawabinsa, Abdulazeez Abdullahi, Shugaban qnungiyar xalibai ‘yan asalin Abuja (AISA), ya yaba wa shugaban bisa wannan karimcin da ya nuna masu.

Ya yi alqawarin cewa xaliban a nasu vangaren za su ci gaba da kasancewa kyawawan jakadu na qaramar hukumar a duk inda suka samu kansu.

Xaya daga cikin waxanda suka ci gajiyar shirin akwai, Ayuba Ishaya, xalibin MSc, ya gode wa shugaban makarantar bisa wannan tallafin karatun nasa, tare da jaddada cewa hakan zai taimaka matuqa wajen taimaka wa karatun nasa.

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply