Shugabannin PDP A Edo Sun Bukaci Magoya Bayansu Da Su Fito Kada Kuri’a Ranar 19 Ga Watan Satumba

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Jam’iyyar PDP a Edo ranar Talata ta bukaci magoya bayanta da kada su tsorota da ayyukan wasu ‘yan siyasa, su fito don kada wa  jam’iyyar kuri’a a ranar 19 ga watan Satumba.

Jam’iyyar ta yi kiran ne a babban gangamin da ta shirya don zaben Gwamnan da za a yi ranar Asabar.

Dakta Tony Aziegbemi, Shugaban jam’iyyar a jihar, ya nemi su fito kwansu da kwarkwatarsu don kada wa dan takarar PDP, Godwin Obaseki kuri’a.

Ya basu tabbacin cewar za a kirga kuri’arsu.

 

Shi a nashi bangaren, Shugaban yakin neman zaben PDP na Edo, Cif Dan Orbih, ya ce sun kewaya gundumomi 192 domin yakin neman zabe, kuma muryar jama’a ta fito sun nuna wa suke so.

Ya yi nuni da cewa wadanda suka zo Edo don goyon bayan wani mutum su sake tunani.

Ya jadadda cewa daga yakin neman zaben da suka fito, sun fahimci cewar al’ummar Edo sun shirya cewa sai an kirga kuri’arsu.

Ya kuma kara da cewa wadanda suke tunanin wani karfi, ya kamata su fahimci PDP da dan takararta na “da goyon bayan Allah da jama’a”.

Sanata Matthew Uroghide, mai wakiltar Edo ta Kudu ya ce abin da ya fito fili shi ne dan takarar PDP na da goyon bayan jama’ar Edo.

A nashi bangaren, Cif Tom Ikimi, wani jigo a jam’iyyar ya yi nuni da cewa ‘yan Edo sun shirya tsaf don ganin an sake zaben PDP da dan takararta ranar Asabar.

Cif Raymond Dokpesi, wanda ya yi jawabi a matsayin shugaban Edo ta Arewa ya ce abin takaici ne a ce  dan yankinsu na aiki tukuru don tsayar da jirgin ci gaba a jihar.

 

Share.

About Author

Leave A Reply