Siyasa: Tsohon Gwamnan Adamawa, Ngillari Ya Fice Daga PDP Zuwa APC

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Tsohon Gwamnan Adamawa karkashin jam’iyyar PDP, James Ngillari, ya sauya sheka zuwa APC.

 

Alhaji Ibrahim Bilal, Shugaban jam’iyyar APC a jihar ne ya bayyana haka ranar Asabar a Yola.

 

Bilal ya yi bayanin cewa tsohon gwamnan na PDP ya fice daga jam’iyyar ne tare da dubban magoya bayansa.

 

“Ina son na yi amfani da wannan damar wajen sanar da ku cewa tsohon Gwamnan jihar nan karkashin PDP, James Ngillari, ya sauya sheka zuwa APC.

 

“Ngillari ya koma APC ne bayan shawarwari, kuma ya dawo jam’iyyar ne da dubban magoya bayansa.

 

“Ya fada min baki da baki cewa zai dawo APC ne ba wai don neman shugabanci ba, sai da don ribatar ‘yancin siyasa,” inji Ibrahim Bilal.

 

Shugaban jam’iyyar ya ce APC a matakin kasa da kuma jiha na kokarin shirya bikin yi wa gwamnan na PDP da magoya bayansa wanka.

 

Ya ce jam’iyyar a matakin jiha na nan na tattaunawa da kwamitin Mai Mala don karfafa jam’iyyar don zaben 2023.

 

Share.

About Author

Leave A Reply