Sojoji Sun Ceto Wani Dalibi Da Aka Yi Garkuwa Da Shi A Jihar Filato

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Rundunar ta musamman na dakarun sojojin Nijeriya mai suna ‘Operation Safe Haven (OPSH)’ wadanda ke kula da sassan jihohin Filato da Kaduna da kuma Bauchi sun samu nasarar ceto wani dalibi da aka yi garkuwa da shi.

Dalibin mai suna, Mr Kelvin Eze, yana karatu ne a ‘King’s College, Gana Ropp, da ke karamar hukumar Barkin Ladi ta jihar flato, an kuma sace shi ne a ranar 29 ga watan Afrilu na wanan shekarar.

Jami’in watsa labarai na rundunar, Maj. Ibrahim Shittu, ya sanar da haka a takardar sanarwa da aka raba wa manema labarai a garin Jos ranar Lahadi.

Ya ce, an samu nasrar ceto dalibin ne a ranar 1 ga watan Mayu da misalin karfe 8:35 na dare.

A ranar 29 ga watan Afrlu ne ‘yan bindiga suka mamaye makarantar inda suka yi awon gaba da dalibi daya.

Sai dai bai kuma bayyana a ina aka ceto dalibin ba amma ya ce, an ceto shi ne ba tare da ji masa ciwo ba ba a kuma biya wani kudin fansa ba kafin a sako shi.

Ya kuma yi bayanin cewa an samu nasarar ne bayan da dakarun suka yi bincike mai tsananani a yankin da ake zaton barayin su voye shi.

Ya kuma tabbatar wa al’umma cewa, rundunar za ta cigaba da tabbatar da tsaron lafiyar al’umma tare da kare dukiyarsu, ya kuma bukaci al’umma su cigaba da bayar da hadin kai ga rundunar don tabbatar da wannan nasarar.

Share.

About Author

Leave A Reply