Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Biyu A Kaduna

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Jami’am tsaro na rundunar ‘Operation Thunder Strike’ sun samu nasarar kashe ‘yan ta’adda biyu a wani kwantan baunar da aka yi wa ‘yan ta’addan a yankin Gwagwada-Chikun da ke karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro cikin gida na jihar, Mr Samuel Aruwan, ya sanar da haka a takardar manema labarai da ya sanya wa hanun aka kuma raba wa manema labarai a Kaduna ranar Asabar.

Ya kuma kara da cewa, “Mun samu labarin yadda dakarunmu suka samu nasarar kashe ‘yan ta’adda a wani kwanto baunar da aka yi musu.

“’Yan ta’addan na tafe ne a kan mashina su biyu daga nan ne jami’anmu suka yi musu kwanton bauna inda suka kashe su gaba daya.

Ya kuma bayyana cewa, bayan da kura ta lafa an samu mashin daya da bindigar gida daya da kuma wayar hannun da kuma sinkin tabar wiwi tattare da gawar yan ta’addan.

Kwamishin ya kuma ce, Gwamna Nasir El-Rufai ya taya dakarun murnar wanna nasara5r da suka samu ya kuma bukaci su cigaba da fafatawa day an ta’adda har sai an ga bayan su a jihar.

“An na kra ga al’umma su sanya ido akan suk wanda suka ga yana meman magani na harbij bindga da aka yi msa, su kima gaggauta kai rahoton zuwa jami’an tsaron da ke kusa.

Share.

About Author

Leave A Reply