Soki Burutsun Masu Sukar Farfesa Gambari, Daga Gidado Ibrahim

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Tabbatar da nadin Farfesa Gambari a matsayin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati ya nuna bangarorin mutane biyu. A dai dai lokacin da mafi rinjayen ‘yan Nijeriya ke murna da nadin wannan shahararren malami, ma’aikaci, masanin diflomasiyya kuma malami wasu kuma sun ba kansu aikin soki burutsu domin dauke hankalin wannan gogaggen ma’aikacin da ke gab da kama aikin hidimtawa Shugaba Buhari.

Duk da yake kowanne mutum na da ikon bayyana ra’ayinsa, sai dai yana da kyau a fahimci cewa wannan ba dalili ba ne da mutum zai rika yawo da rashin mutunci da iya shegen da ka iya zama barazana ga wanzuwar Nijeriya. Kuma bin haushin masu irin haka sune fa wadannan ‘yan Nijeriyan da a baya suka yi watanda da makomar kasar, sune a yau suke sukar wasu da duk wani nau’in soki burutsu.

Su fa wadannan mutanen, yana da kyau a fahimci cewa babban burinsu shi ne su rikirkita duk wani abu da Shugaba Muhammadu Buhari ya sa a gaba. Babu ruwansu da kokarin gyara da yake yi. A sani cewa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya riga ya shiga ran ‘yan Nijeriya, sun yarda da shi don haka babu wani abu da magauta za su iya yi su bakanta shi.

Da yawan ‘yan Nijeriya sun yabawa hangen nesan Shugaban Kasa Buhari wurin zabo Gambari a matsayin Shugaban Ma’aikatansa. Bari na fada muku abin da masana ke fadi dangane da wannan nadin, sun ce: wannan shi ne mafi kololuwar cancanta a nade-naden da Shugaba Buhari ya yi.

Wa ye muke bukata a irin wannan yanayi na rikirkicewar al’amura, fiye da mutumin da ke da kwarewa irin Gambari, wanda duk ya cika dukkanin sharudda na sanin makamar aiki, ga dabi’a mai kyau da kuma gaskiya. Mutum ne da ke da abokai masana a duk fadin duniya.

A kokarinsu na son kawo hayaniya, sun koma yanzu suna kirkiro bayanai daga gwamnatocin baya, duk da zimmar sai sun haifarwa da Farfesa Gambari cikas.

Yana da kyau a rika tunani, ta yaya kamfen din Napoleon Bonaparte ya taba tasirin Faransa a yammacin turai? Su wadanda ke dauko abubuwan shekarun baya suna bukatar likitan kwakwalwa. ‘Yan Nijeriya na bukatar aiki ne a yanzu ba kirkiro tarihin karya ba.

Sai kuma me? Ban ga wani abu ba don Farfesan da ya shekara 30 a matsayin masani ya yi gyara ga matashin dan jarida kan yadda ya kamata ya rika amsa tambayoyi. Ko muna nufin Dan jarida Seun Akibaloye 10 yake cif-cif? Wannan abin da suke yi ya fi kama da a ba Kare sunan banza don a rataye shi. Idan ba haka ba, ta yaya Farfesa Gambari da duk duniya ta sanshi don ya yi wad an jarida gyara ya zama tsegumi?

Baya ga kasantuwarsa ministan kasashen waje a shekaru 35 da suka gabata, Sannan kuma wakilin Nijeriya a Majalisar Dinkin duniya, Farfesa Gambari ya yi gogayya da mashahuren ‘yan jarida a fadin duniya. Don haka yana da ikon daidaita dan jarida a yayin da ya so ya kauce hanya.

Sai dai ko muna son bin ranmu, amma lokaci ya yi da ya kamata mu daina kawo abin da babu shi. Mu fadawa kanmu gaskiya, wadannan abubuwan sam basu da wata fa’ida ga Nijeriya. Idan ba haka ba, wanne mutum mai hankali ne zai kawo batun wai Farfesa Gambari ya goyi bayan Janar Abacha wurin kisan Ken Saro Wiwa da wasu? Ganin yadda duniya ta yi caaa ga kashe-kashen na shekarar 1995, ta yaya Farfesa Gambari ya samu karbuwa da mutunci a idon duniya, idan har da hannunsa a wadannan abubuwan? Daga kin gaskiya sai bata. Wadanda ke yawo da irin wannan mutane ne dake fuskantar shari’a kan cin hanci da rashawa. Su ne ke son su yamutsa hazo.

A cikin wadanda ke wannan soki burutsu wane ne ke da takarda da kwarewar Farfesa Gambari? Wanene a cikinsu ke da dabi’a da saninsa? Wanene ke da sanayya a fadin duniya kuma wanda za a iya dogaro da shi? Zan fadi da babbar murya, lokacin cin mutuncin babban ma’aikacin gwamnati don neman kudi ya wuce. Abin kuma da ya kamata su sani shi ne a fadin duniya yanzu babu wani shugaban ma’aikatan fadar gwamnati da ke da gogewar da namu na Nijeriya ke da shi.

Ba ruwansu da gogewarsa, wasu sun dauki nauyin sojojin baka da aikinsu a yanzu shi ne batanci ga Farfesa Gambari. Sun ware kudade suna daukar nauyin jaridu da marubuta wurin ganin tarwatsa kimar wannan farfesa da ya kwashe shekaru yana ginawa. Mu taru mu yi yekuwar sanar da mutanen nan cewa yanzu wannan lokacin na babarodo da cin mutunci ya wuce.

Wadanda ke wannan soki burutsu sune mutanen da tsohon Kakakin tsohon shugaban kasa, Dakta Reuben Abati ya ambata da: “Babbar barazana ga masu fashin baki a wannan zamani shi ne mun samu tarin mutane marasa kan gado suna tofa albarkacin baki, kuma ana samun masu ilimi suna biye musu.”

A irin hidimar da ya yi wa kasarsa, lokacin yana ministan kasashen waje a tsakanin 1984 zuwa 1985, a zamanin mulkin soja na Buhari, Farfesa Gambari ya yi aiki babu kama hannun yaro. Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon ya nada shi a matsayin shugaban kula da sashen kasashen Afirka na wakilan Majalisar Dinkin Duniya a Darfur a shekarar 2010.

Haka kuma ya yi aiki a matsayin mai ba shugaban majalisar dinkin duniya shawara kan lamurran Iraki.  A duk wadannan ayyuka da Gambari ya yi ba a taba samunsa da rashin gaskiya ko wani laifi ba.

Mutum mai irin wannan tarin mutunci da kwarewa, babu wani mafi cancanta da wannan kujera ta shugaban ma’aikatan fadar gwamnati fiye da Farfesa Gambari. Abin kawai da ake bukata a yanzu shi ne hadin gwiwa da bayar da hadin kai wurin ganin wannan bawan Allah ya cimma nasara.

–      Ibrahim shi ne Daraktan Sadarwa da tsare-tsare na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa (Presidential Support Committee)

 

Awesome
  • User Ratings (0 Votes) 0
Share.

About Author

Leave A Reply