Sudan Ta Zargin Habasha Da Karya Yarjejeniyar Kare Iyakokin Kasar

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Ranar Laraba ne Hukumar kare iyakokin kasar ta Sudan ta zargi Habasha da keta yarjejeniyar kan iyakokin da aka sanya hannu tsakanin kasashen biyu.

An ruwaito cewa, shugaban hukumar, Maaz Tango, ya yi wa jakadu, da jami’an diflomasiyya, da wakilan kungiyoyin yanki da na kasa da kasa bayani game da rikicin kan iyaka tsakanin kasashen biyu a taron da aka yi Tango.

Habasha ta kuma kauce wa wajibanta a kan yarjejeniyar kan iyakokin wadanda za a iya gano su tun farkon shekarar 1903, in ji shi.

A cewar jami’in na Sudan din, kasarsa na da dukkan takaddun da ke nuna goyon baya ga matsayinta da ‘yancinta kan filayen da Sojojin Habasha suka shiga.

A safiyar yau, ma’aikatar harkokin wajen Sudan ta ce wani jirgin saman sojan Habasha ya kutsa kan iyakar Sudan a abin da ta kira “mummunan ci gaba da rashin dacewar”.

Tun daga watan Satumban shekarar 2020, iyakar Sudan da Habasha ta fara fuskantar tashin hankali da fadace fadace tsakanin bangarorin biyu.

Yankin kan iyaka na Fashaga tsakanin Sudan da Habasha, daya daga cikin kananan hukumomi biyar na jihar Gadaref ta Sudan, galibi ya kan shaida munanan hare-hare daga ‘yan bindigar Habasha yayin shirye-shiryen lokacin noman.

Share.

About Author

Leave A Reply