Sultan Ya Umarci A Fara Duban Jaririn Watan Ramadan Daga Gobe Litinin

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Mai Alfarma Sultan na Sakkwato, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya umarci al’umma Musulmi su fara duban jaririn watan Ramadan daga ranar Litinin 12 ga watan Afrilu 2021.

A ranar Lahadi Sultan ya bayar da umarnin a takardar sanarwa da shugaban kwamitin bayar da shawara kan harkokin addini na masarautar, Farfesa Sambo Junaidu, ya sanya wa hannu aka kuma raba wa manema labarai a garin Sakkwato.

“Muna masu sanar da al’umma Musulumi da cewa, ranar Litinin 29 ga watan Sha’aban 1442 wanda ya yi daidai da ranar Litinin 12 ga watan Afrilu zai kasance ranar da za a fara duba watan Ramadan na shekarar 1442AH.

Akan haka muke umartar al’umma Musulmi da su sa ido don duba watan su kuma sanar a hukumar mafi kusa dasu wanda kuma za a mika sanarwa zuwa ga Sultan don a sanar da al’umma Musulmi gaba daya,’’ inji sanarwar.

Sultan ya kuma yi addu’a Allah ya taimaka mana wajen sauke nauyin addini da ke a kan mu.

Farfesa Junaidu ya kuma bayar da lambobin wayar da za a yiamfani dasu wajen isar da sakon zuwa ofishin Sultan, mambobin sun hada da 08037157100, 07067416900, 08066303077, 08036149757, 08035965322 da kuma 08035945903.

 

Share.

About Author

Leave A Reply