Tattaunawa: Dr. Dauda Lawal Dare Zai Dauki Nauyin Karatun Dalibai Daga Zamfara Zuwa Togo

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Wannan ita ce hirar da aka yi da tsohon Babban Daraktan Bankin First Bank kuma dan takarar gwamnan Jihar Zamfara a karkashin inuwar jam’iyyar APC a zaben 2019, DR. DAUDA LAWAL DARE. An yi hirar ne a ranar Sallah Karama wanda ya yi daidai da 13 ga watan Maris din 2021.

Ko za ka gabatar mana da kanka, da dalilin ziyarorin da ka kai ranar Sallah?

Sunana Dr. Dauda Lawal. Yau rana ce, ranar murna, ranar farin ciki a garemu da Allah Ya nuna mana wannan rana da muka gama azumi na watan Ramadan cikin koshin lafiya.

Kamar dai yadda ka sani ne, rana ce da ake ziyarar ‘yan uwa da abokan arziki don a yi murnar wannan rana da Allah Ya nuna mana, don ba kowa ke da wannan gatar ba, don akwai wadanda mun fara azumi da su, amma yau babu su. Kamar yadda na ce ne, ranar murna ce da za ka ziyarci ‘yan uwa da abokan arziki.

Kuma kamar yadda muka yi yau, na je Talatar Mafara, inda na ziyarci tsohon gwamna, Dr. Abdul’aziz Yari. A hanyar dawowa na tsaya a garin Maru inda na ziyarci fadar Mai Martaba Sarkin Maru, shi ma na yi masa gaisuwar sallah. Daga nan na tsaya a Bungudu, shi ma na ziyarci Sarkin Fulanin Bungudu. Yanzu kuma ga shi na dawo gida cikin garin Gusau ina ganin ‘yan uwa da abokan arziki inda nake yi musu barka da sallah.

Yau dai Kasar nan, kamar yadda duka muka sani, muna cikin wani hali na kaka-nika-yi, ta hanyar tsaro, tattalin arziki, kiwon lafiya da makamantansu. Abu ne da zan ce dole mu tashi da addu’a. Wadannan masifofi da muke fama da su a Nijeriya da a Jihar Zamfara, Allah Ya kawo mana saukinsu. Allah Shi Ya san daidai, kurakuren da muka yi Ya yafe mana, amma dole ne sai mun yi addu’a don neman sauki daga wurin Allah (T).

Wacce gudummawa ka ke ba gwamnati mai ci don kawo karshen matsalar tsaro a Jihar Zamfara?

Kamar dai yadda aka sani, Zamfara jihata ce. Ba ni da wata jiha da ta fi Zamfara, saboda haka abu ne ba wai lallai na maganar siyasa ba, abu ne da ya shafi kowa. Idan ka duba tsaro muna cikin wani hali, idan ka duba tattalin arziki muna cikin wani hali. Shi gwamna Matawalle abokina ne, kuma lokaci bayan lokaci na kan tuntube shi, shi ma yaka tuntube ni don ganin yadda za a shawo kan wadannan matsaloli na tsaro, na tattalin arziki, na ilimi da sauransu, don mu ga ta inda za mu samu mafita. Kuma wannan wani abu ne da za mu ci gaba da yi, ba wai na lokaci daya ba. Duk lokacin da muka ga wani abu wanda ba daidai ba, za mu yi kokari mu janyo hankalin gwamna mu ba shi shawara. Kuma na san idan muka ci gaba da yin haka, tare da rook Allah za mu samu mafitan wadannan matsaloli.

Shin ya ka ji yayin da wata Jami’a a Kasar Togo ta karrama ka?

Toh, ka san kowa aka ce an karrama shi, abu ne na murna da farin ciki. A gaskiya na yi murna, na yi farin ciki, na kuma godewa Allah da wannan karamci da wannan jami’a ta Kasar Togo ta yi min. Cikin abubuwan da muka tattauna shi ne yadda za su taimaka, ni ma kuma na taimaka wurin ganin mun samar da guraben karatu ga ‘yan asalin jiharmu ta Zamfara a wannan jami’ar. Yanzu haka muna nan mun shirya wannan fom din, zan yi magana da dukkanin ko’odineto dina a zagaya kananan hukumomi cikin 14 da muke da su a Zamfara don ganin an yi wannan tsari na taimakawa al’ummarmu.

Wanne sako ka ke da shi zuwa ga al’ummar Jihar Zamfara?

Sako na ga al’ummar Jihar Zamfara ina yi musu barka da sallah, ina kuma so zu ci gaba da kasancewa masu gaskiya. Don mu yi aiki don ganin yadda za mu shawo kan matsalolin tsaro, ilimi, kiwon lafiya da sauransu. Abu ne wanda dole ne mu hada kai, ba ma don siyasa ba, don ci gaban jihar. Kuma na yi Imani idan muka yi haka, abubuwa za su daidaita.

 

Share.

About Author

Leave A Reply