TETFund, Binciken Kimiyya Da Ajandar Buhari Ta Zango Na Gaba, Daga Gidado Ibrahim

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A wannan karon ma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da muradin gwamnatinsa na son fitar da sama da mutum miliyan 100 daga talauci. Wannan, babu makawa abu ne da zai yiwu bisa la’akari da irin abubuwan da gwamnatin ta sa a gaba.

Misali idan muka kalli kasar Chana, wacce ta iya fitar da mutum miliyan 700 daga talauci a cikin shekara 40, za mu iya cewa lallai Nijeriya za ta iya cimma wannan muradi na ta. Don haka dole ne a bi matakan da suka dace wurin ganin an cimma nasara. Daga cikin muhimman hanyoyin da Chana ta bi shi ne yin tattali a bangaren kimiyya, ta hanyar kirkire a fannin binciken kimiyya.

Hukumar TETFunda karkashin jagorancin Farfesa Suleiman Elias Bogoro bisa daidaito da ajandar gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta samar da shirin tallafawa ilimi domin ta karfafa masu son yin binciken kimiyya. Fiye da sauran lokuta na baya, wannan zamani ne da ake bukatar bunkasa binciken kimiyya. Wannan shi ne dalilin da ya sa dole a jinjinawa shirin TETFund na bunkasa binciken ilimi ‘Educational Research Development’ wanda Farfesa Bogoro ya samar.

Domin ganin wannan kuduri ya kai ga nasara, hukumar TETFund ta fara aiwatar da wannan shiri na tallafawa bunkasar binciken kimiyya, wanda shi ne zai zama tamkar ‘yar manuniya ga yunkurin gwamnati.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nuna a shirye yake ya zartas da shawarar hukumar gudanarwar TETFund ta bayar na a kara kudin binciken kimiyya da TETFund din ke warewa daga Naira Biliyan 5 a shekarar 2019 zuwa Naira Biliyan 7.5 a shekarar 2020.

Wannan wani shiri ne da zai taimakawa Nijeriya wurin gaggawar bunkasa kamar sauran kasashen duniya a fannin ilimi. Babu ko tantama, Farfesa Bogoro ya dau turbar farfado da kudurin gwmanatin tarayya domin bunkasa fannin binciken kimiyya.

Wasu daga cikin fannonin da TETFund ta fi mayar da hankali akwai binciken da ke nemo mafita ga matsalolin kasa, a bangarorin da suka shafi Tsaron Kasa, Hadin kan kasa, zaman lafiya, ilimi da horaswa, Bunkasar tattalin arziki, noma, bunkasar fasaha, wutar lantarki da sauransu.

Shi wannan bincike makasudinsa shi ne a samar da yanayin da zai ciyar da makarantun gaba da sakandare gaba. Bincike ne da zai mayar da hankali akan dukkanin fannonin ilimi da ake da su. Tsarin wanda a turance ke yi masa take da ‘Intitution-based research (IBR)’ tabbas zai farfado da binciken kimiyya a jami’o’i da sauran makarantun gaba da sakandare.

A jawabinsa yayin kaddamar da wannan shiri, Shugaban Hukumar TETFund, Farfesa Elias Bogoro ya yi bayanin irin bukatar gaggawa da ake da ita ga daukaka binciken kimiyya da bunkasar ilimi. Ya nuna matukar damuwarsa kan yadda a ka dauki lokaci mai tsawo ba tare da an muhimmanta wannan fili na binciken kimiyya da bunkasar ilimi ba, wanda hakan ya janyo nakasu sosai a harkar ilimin Nijeriya.

Haka nan kuma Farfesa Bogoro ya jinjina tare da yaba wa Shugaba Buhari dangane da irin gudummawar da yake ba bunkasar ilimin kimiyya. musamman ma batun yin kari  kudin binciken kimiyya da kaso 50 da gwamnatin Buharin ta yi a shekarar 2020.

Babbar nasarar bunkasar fannin ilimi shi ne ya zama an iya magance matsalar tsarin bincike na ilmi an kuma taimakawa masana ta hanyar basu dama su gudanar da bincike yadda ka’idar kimiyya ta tanada. A dalilin haka ne ya sa aka samar da Hukumar TETFund a Nijeriya. Ba kamar a shekarun baya ba, a yanzu lokacin shugabancin Farfesa Elias Bogoro ya sauya hukumar daidai da wannan aiki da aka kafa shi dominshi.

Kamar yadda Shugaban na TETFund ya fadi ne, babban dalilin shirin binciken kimiyya da bunkasar ilimi shi ne a shigar da tsarin cikin dokokin Nijeriya, wanda zai taimakawa jami’o’in Nijeriya wurin shiga sahun gaba – gaba a jami’o’in duniya. Zai kuma taimaka wurin samar da ayyukan yi da daman gaske a Nijeriya.

A yanzu dai gwamnatin Buhari ta nuna da gaske ta ke yi wurin ganin wannan shiri ya cimma nasara. Amma duk da haka, Shugaban TETFund, Farfesa Bogoro ya ce, saboda yawan da jami’o’in da ake da su, akalla ana bukatar dala biliyan daya duk shekara wurin gudanar da wannan aiki.

A makon da ya gabata mun ga yadda membobin Majalisar Tarayya suka ayyana aniyarsu ta ba wannan shiri na Binciken Kimiyya da Bunkasar ilimi hadin kai dari bisa dari, ta yadda za a zamanantar da shiirin a kuma shigar da shi cikin doka.

Matukar muna so mu ga haske da kuma ci gaba mai dorewa, kamar yadda Farfesa Bogoro ya fadi ne, dole ne mu muhimmantar da sashen kimiyya da fasaha, ba kamar yadda muke yi wa sashen rikon sakainar kashi ba. Gwamnati, malaman jami’a da masu hannu da shuni dole ne su hadu a inuwa daya wurin samar da kirkire-kirkire da binciken kimiyya da fasaha, ta yadda za a rika samar da abubuwan kimiyya a Nijeriya. Duk wani binciken kimiyyan da ba zai samar da hanyar samun kudi ba, ana iya cewa kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.

Dole ne mu hada karfi da karfe wurin ganin mun karfafa wannan shiri mai tarin muhimmanci. Nan ba da jimawa ba za a kaddamar da wannan shiri, wanda zai samu sa albarka daga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu.

– Ibrahim Shi ne Daraktan Sadarwa da Tsare-tsare na Kwamitin Tallafawa Shugaban Kasa (PSC).

Awesome
  • User Ratings (0 Votes) 0
Share.

About Author

Leave A Reply