Tinubu Ya Bukaci Matasa Su Nisanci Bangar Siyasa

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci matasan yankin Agege dama na fadin jihar Legas gaba daya dasu rungumi tafarkin zaman lafiya tare da nisantar harkokin bangar siyasa.

A ranar Juma’a ne Tinubu ya bayar da wannan shawarar a yayin kaddamar da gadar sama mai nisan kilomita 1.4 da ke Pen Cinema junction, Agege. Ya nemi matasan rungumi zaman lafiya don ita ce hanyar cigaba a rayuwa.

Ya kuma ce, sai da zaman lafiya za a samu dukkan cigaba akan haka ya kamata a rungumi zaman lafiya a dukkan lokutta.

Jagoran jam’iyyar ya kuma yaba wa gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, da ‘yan majalisarsa akan cigaba da suka kawo wa jihar.

Ya kuma jinjina musu akan yadda suka fuskanci lamarin annobar cutar korona da kuma matsalar zanga zanga EndSARS.

”Maimakon rudewa tabbas kun tsayu kuma kun yi aiki yadda yakamata duk da matsalolin da aka fuskanta.

Share.

About Author

Leave A Reply