Tsakanin Kishin Nijeriya Da Masu Yekuwar Buhari Ya Yi Murabus, Daga Gidado Ibrahim

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

A lokaci na Dimokradiyya, musamman wanda aka kwaikwayo tsarin dimokradiyyar Amurka, an yi bayanin yadda ake zaben Shugaban Kasa, da kuma idan bukatuwar hakan ta samu, yadda Shugaban Kasa ke ajiye aiki. Ana fara maganar yin murabus din shugaban kasa ne a yayin da Shugaban ya gaza a wurin sauke nauyin da ke kansa kamar yadda kundin tsarin mulki na shekarar 1999 ya tanada. Wannan kuma bisa sharadin shugaban na fama da walau rashin lafiya ko hauka.

Akwai ban takaici da ban haushi ganin yadda duk da wannan shiri na kundin tsarin mulki, wasu baragurbi a ‘yan kwanakin nan suna ta yekuwar wai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi murabus. Wadannan mutanen sun dauka a komi ne sai sun sa siyasa, shi ne ma ya sa suke kira ga shugaban kasa da ya ajiye aiki. Suna fakewa da batun rashin tsaro da ake fama da shi a fadin kasar wurin son cimma mummunar manufarsu.

Yekuwar Buhari ya yi murabus ba komi ba ne face son rai da hassada. Shugaban Kasa dai lafiyarsa lau kuma shi ne ke tafiyar da lamurran Kasar. Tambayar a nan ita ce, mene ne dalilin wannan kira nasu? Amsar daya ce, cewa wasu lalatattun ‘yan siyasa ne suka dauki nauyinsu. Damuwarsu ita ce Buhari ya toshe duk wata kafa da hanyar satar kudin gwamnati. Buhari ya datse hanyoyin dandatsar kudin gwamnati tare da karkatar da wadannan kudade zuwa ga ayyukan raya kasa da hidimtawa jama’a.

Haka nan kuma yin yekuwar a tsige shugaban kasa, ba wai kawai abin ban haushi ba ne, akwai rashin hangen nesa. Ta ya ma za a ce wai wata kungiya na yekuwar Shugaban Kasa ya yi murabus a tsarin dimokradiyya? Wadannan mutanen an dauki nauyinsu ne domin kare muradin banza.

Wadannan maganganun banza da kiraye-kirayen kawai da wasu ke yi ta hanyar yin amfani da siyasa da lamarin tsaro ba zai haifar mana da da mai ido ba. Bayan mummunan lamarin da ya faru a garin Zabarmari na Jihar Borno ne suka fara wannan yekuwar na murabus din Shugaban Kasa, inda suke fakewa da batun wai Shugaban Kasa ba ya kokari wurin kawo karshen matsalar tsaron da ke fuskantar arewacin Nijeriya. Amma bisa la’akari da irin kokarin da shugaban kasa Buhari ke yi a fannin tsaro za a fahimci manufar wadannan mutane.

Da bakunansu suka ce a kasashen da suka ci gaba, idan shugaba ya gaza cimma nasarori, abu mafi kima gareshi shi ne ya ajiye aiki. Amma sun gaza kawo kasa guda daya da shugaban kasarta ya yi murabus saboda matsalar tsaro da take fuskanta. Akwai takaici yadda mutane za su fito suna bayyana abubuwan shirme da karairayi kan abin da ba su sani ba, ko kuma su rika yi da gangan. Sai dai har yanzu ba a yi latti ba ai, ‘yan Nijeriya na zaman jiransu su fito su fada mana kasar da aka taba samun afkuwar haka a yankin Turai, Asia, ko Amurka. Muna dai ganin yadda a ke yin adawa a kasashe irinsu Faransa, Kanada, Italiya, Jamus, Rasha da Ingila. Amma a Nijeriya abin ba haka ya ke ba.

Ta bayyana cewa a Nijeriya ne kawai irin haka ke iya faruwa. Inda wata kungiya za ta bayyana da rana tsaka ta fara yin kira ga Shugaban Kasa da ya yi murabus. Wannan ai ba ma ka bukatar a ce maka daukar nauyinsu aka yi.

A lokaci irin wannan, abin da ya kamaci duk wani mai hankali shi ne ya bayar da hadin kai wurin shawo kan matsalar da ake ciki. Akwai karin maganar da ke cewa, idan ka ga Kwado yana rawa a saman ruwa, toh makadinsa na kasan ruwan. Su wadannan baragurbin sun san fa kowacce kasa tana da nata irin matsalolin, amma su ba su fitowa su cewa shugabansu ya yi murabus. Sai dai su taimaka da shawarwari da bayanai na hikima da za a shawo kan matsalar. A nan, abin da za mu fahimta shi ne, wani ko gungun wasu mutane ne ke daukar nauyin wadannan baragurbin mutane.

Rashin hankalin wadannan mutane ba zai bari su fahimci cewa hatta Amurka wacce ita Nijeriya ke kwaikwayo a tsarin gudanarwar mulkinta, sun taba samun yakin basasa, da kuma harin ta’addanci irin na 11 ga watan Satumbar 2001. Ba a taba samun wani lokaci da Amurkawa suka fito suna yekuwar Shugaban Kasa ya yi murabus ba. Maimakon haka, sai ya zama a kowanne lokaci na tsanani za ka taras da Amurkawa na ayyana goyon baya ne ga shugabanninsu don a kawo karshen lamarin.

Idan muka duba hanyar da Nijeriya ta keto daga lokacin da aka samu ‘yancin kai, da irin sadaukarwar da nagartattun mutane suka yi, wannan yekuwar na Shugaban Kasa ya yi murabus tamkar kokarin yi wa dimokradiyya kafar Angulu ne.

Abin haushi hatta kungiyar CNPP da ya kamata a ce ta san daraja da kimar Dimokradiyya, wai har da ita a ke yekuwar Shugaban Kasa ya yi murabus. Dole ne ‘yan Nijeriya su tsaya akan dugaduginsu don kar su bari wadannan lalatattu su jefa su cikin wani hali.

Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba za ta taba yin wasa da lamarin tsaro ba, wanda shi ne abu na farko a ajandarta. Ba a taba yin gwamnati a Nijeriya da ta zuba kudi da karfinta kan tsaro ba irin gwamnatin Buhari. Abin da a ke bukata daga ‘yan Nijeriya shi ne bayar da goyon baya ga wannan kokari na gwamnatin Buhari domin a kai ga tudun mun tsira.

– Ibrahim shi ne Shugaban Riqo na Kungiyar Kamfen Xin Buhari (BCO)

Share.

About Author

Leave A Reply