Tsofaffin Sojoji Sun Nemi Karin Kudin Fansho

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Kungiyar tsofaffin sojoji ta kasa reshen jihar Anambra ta bukaci gwamnatin tarayya ta dubi halin da ake ciki na tabarbarewar tattalin arziki ta kara wa tsofaffin sojoji kudaden fanshon su.

Shugaban kungiyar na jihar Anambara Maj.- Gen. Benedict Agbogu, ya bayyana haka a taron tunawa da mazan jiya na wannan shekara 2021 da aka gudanar a filin wasa na Alex Ekwuene da ke garin Awka ranar Juma’a.

Agbogu ya ce, ya kamata a kara musu kudin fansho don kuwa da zaran an kara wa sojojin da ke bakin aiki albashi nan da nan ake kara kudin ababen masarufi da sauran kudaden harkokin rayuwa wanda hakan ke kara jefa su cikin matsalar rayuwa.

Ya ce, yawancin matan da mazajensu suka mutu da yaran su na shiga cikin mawuyacin hali saboda mutuwar mai samar musu da kudaden.

Ya kuma nemi gwamnatin tarayya da kuma na jihohi da su tallafa wa kungiyar ta yadda za su iya taimaka wa iyalan sojojin da suka mutu a fagen fama.

“Gwamnati na kokari amma ya kamata gwamnati ta kara kaimi, muna fatan abubuwa za su gyaru anan gaba kadan.

“Muna magana ne akan mutanen da suka bayar da rayuwarsu don kasar ta kasance a matsayin tsintsiya madaurunki daya, akan haka muke fatan za su kula da mu yadda yakamata.

A nasa jawabin, gwamna Willie Obiano na jihar Anambara ya yaba wa sojoji kan yadda suka bayar da rayuwarsu kan tabbatar da kasar nan.

 

 

 

Share.

About Author

Leave A Reply