Umar Mohammed, EFCC Da Bukatar Hadin Kai, Daga Gidado Ibrahim

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Bincike ya nuna cewa ilimin sanin ma’aikata yana da matukar tasiri wurin nasarar shugabanci. A lokuta da dama idan aka dauko wani daga waje domin ya jagoranci wata ma’aikata, musamman muhimman ma’aikatun gwamnati irinsu EFCC.

A duk fadin duniya, kasashe suna muhimmanta lura da tattalin arziki a ma’aikatu ta yadda za a dakile yiwuwar cin hanci da rashawa. Tun bayan samar da Hukumar EFCC a shekarar 2003, da kuma zartas da ita a matsayin doka daga majalisar kasa, an yi ta kokarin bin hanyoyin rage kaifin cin hanci a Nijeriya.

Sai dai, in dai har kokarin da ake ta yi tun daga shekarar 2004 zuwa yau ba a samu abin da ake so, kenan akwai bukatar a yi la’akari da bayar da dama ga mutumin da ya san ciki da wajen hukumar domin yin abin da ya kamata.

Wannan ya isa ya nuna irin hangen nesan da ke cikin nada Mohammed Umar a matsayin shugaban riko na Hukumar EFCC wanda shugaba Buhari ya yi. Tunda an tsinci kai a wani hali wanda dole ta sa an tsige tsohon Shugaban Hukumar, Ibrahim Magu, dole shi ya sa Shugaba Buhari ya aike ma majalisa da sunan Mohammed Umar.

Domin fayyace komi, Hukumar EFCC bangaren tsaro ne a Nijeriya wacce ke lura da ayyukan cin hanci da rashawa, damfara da sauransu. Dama wannan shi ne dalilin kirkirar hukumar ta cin rashawa.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar 9 ga watan Nuwamban 2015 ya nada Ibrahim Magu a matsayin shugaban riko na hukumar. Sai dai Majalisar Dattawan Nijeriya ta ki ta tabbatar da mukamin nasa har karo biyu sbaoda wasu bayanan sirri da suke da su.

Bayan da Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya fitar da wasu bayanai dangane da Shugaban EFCC, Ibrahim Magu sai kwamitin fadar Shugaban Kasa ta shiga bincikensa.

Saboda irin matsalolin cin hanci da rashawar da muke fuskanta a yau, akwai ban takaici a ce shugaban hukumar da ke yaki da wannan annoba irin EFCC, za a rika kawo shi ne daga waje. Amma yanzu ana iya cewa sam-barka, saboda dan gida ne aka ba ragamar.

Idan har an dauki harkar yaki da rashawa da gaske, toh ya kamata ne a bar shugabancin wannan hukuma ta EFCC ga mutumin da ya dade cikinta, ya san ciki da wajenta da irin wainar da ake toyawa. Ai sanin kowa ne idan aka yi wa sabon mutum nadi a ma’aikata, zai dauki lokaci mai tsawo yana nazarin ma’aikatar, wanda kafin a ankara lokaci zai kure.

Idan abin a fadi gaskiya ne, toh tabbatas nadin Mohammed Umar a matsayin sabon shugaban rikon Hukumar EFCC, abin a yaba ne, a kuma taya Nijeriya da ‘yan Nijeriya murna.

Mohammed Umar wanda asalinsa dan Jihar Kano ne, yana da kwarewar da babu makawa zai iya magance matsalolin da ke addabar wannan hukuma ta EFCC. Tabbatas alamu sun nuna dukkanin irin tarin matsalolin da tsoffin shugabannin hukumar EFCC suka fuskanta, Mohammed Umar zai kiyaye afkawa cikinsu.

Karin tagomashi ga Mohammed Umar shi ne, ya kasance mai mukamin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda a rundunar ‘yan sandan Nijeriya. A matsayinsa na mataimakin kwamishina, yana da tarin ilimi da kwarewa akan ayyukan barna da dnagoginsu, haka nan fannin rashawa da cin hanci.

Baya ga kasancewarsa babban dan sanda, ya kuma kasance dan gida a Hukumar EFCC. Kafin a yi masa wannan mukamin, shi ne Daraktan gudanarwa na Hedikwatar EFCC da ke Abuja, wanda ko a iya nan aka tsaya an san an nada mutumin da ya dace domin yin abin da ya dace, a kuma lokacin da ya dace.

Ina iya tuna yadda Mohammed Umar ya yi yaki babu kama hannun yaro da masu zamba cikin aminci a harkar tallafin man fetur da kuma manyan masu damfara ta intanet. Wannan irin kokarin na Mohammed Umar ya yi matukar daga martaba da darajar Nijeriya a idon duniya. A lokacin da yake Daraktan Gudanarwa na EFCC, ya tabbatar da dakilewa tare da hukunta mazambata a harkar man fetur, ta yadda sai da ya daidaita lamurra a wannan bangare.

Wani karin haske shi ne, Mohammed Umar a matsayinsa na na’ibin Magu, tunda a gabada hukumar EFCC, daga Magun sai shi, wannan ya ba shi daman halartar wasu muhimman taruka, a wasu lokutan ma shi ne ke wakiltar Magu ko hukumar. Wannan ya taimaka wurin gina shi a kan aikin da yanzu aka ba shi.

Kamar Ibrahim Magu, idan aka bar Mohammed Umar ya dade sosai a matsayin shugaban riko, hakan zai rage mishi karsashi da zimmar yin aikin. Saboda hake ne ake da matukar bukatar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya turawa da majalisa sunan Mohammed Umar domin su tantance shi ya fara babban aikin da ke gabansa.

Wani abu guda daya da zan tabbatarwa da ‘yan Nijeriya da kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari shi ne, a karkashin shugabancin Mohammed Umar, hukumar EFCC za ta dawo da martabarta da kimarta a matsayin babbar hukumar yaki da cin hanci da rashawa a fadin Afirka ba ma Nijeriya kawai ba.

Ibrahim shi ne Daraktan Sadarwa da tsare-tsare na kwamitin tallafawa Shugaban Kasa ‘Presidential Support Committee’ (PSC).

Awesome
  • User Ratings (0 Votes) 0
Share.

About Author

Leave A Reply